Tsohon Gwamna Ya Yi Wa Peter Obi Tsirara, Ya Tona Gazawarsa a Lokacin Yana Mulki

Tsohon Gwamna Ya Yi Wa Peter Obi Tsirara, Ya Tona Gazawarsa a Lokacin Yana Mulki

  • Adams Oshiomhole yace Peter Obi ba zai iya kawo karshen rashin tsaro da ake fama da shi a kasa ba
  • Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa yace Obi bai iya maganin ‘Yan Bakassi Boys a jihar Anambra ba
  • Oshiomhole yana ganin wanda bai iya tsare jiharsa ba, ba zai iya zama mafita wajen tsare Najeriya ba

Abuja - A ra’ayin Adams Oshiomhole, ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP a 2023 watau Peter Obi, bai san yadda zai magance matsalar tsaro ba.

Daily Trust ta rahoto tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole yana wannan bayani wajen taron da matasan APC suka shirya a garin Abuja.

Oshiomhole yake cewa lokacin da Obi yake gwamna a jihar Anambra, wasu gungunan ‘yan iska da ake kira Bakassi Boys suka hana shi sakat a mulki.

Kara karanta wannan

Baya da kura: Atiku Ya Sheka Kasar Waje, Maganar Shawo Kan Rikicin PDP Ya Wargaje

‘Dan siyasar yace sai da Willie Obiano ya zama gwamnan Anambra sannan aka yi maganin ‘Yan Bakassi Boys da suka gawurta a lokacin Peter Obi yana ofis.

Sharrin ‘Yan Bakassi Boys

Da farko an kafa ‘yan Bakassi Boys ne a matsayin ‘yan banga, amma daga baya sai suka rikide suka koma kashe mutane a kudu maso gabashin Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Wadanda sun gawurta a kafofin sadarwa na zamani, akwai abubuwan da kuke bukatar sani. Ku je kuyi bincike kan watannin farko na Obiano a ofis a Anambra.
Peter Obi
Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Abin da za ku gani a Youtube shi ne yadda Gwamna Obiano ya yi amfani da manyan motoci, ya rusa gidajen masu garkuwa da mutane da ake kira Bakassi boys.
Wanene Gwamna lokacin da Bakassi boys suka yi karfi a Anambra, wanene ya magance matsalar?"
“Mutumin da ya gagara shawo kan matsalar tsaron kasarsa wanda ke bukatar jajircewa, ta ya za a gamsu zai iya magance matsalolin tsaron duka fadin Najeriya?"

Kara karanta wannan

Tun Yanzu, Atiku Abubakar Ya Fara Tattara Sunayen Wadanda Zai Ba Mukamai

- Adams Oshiomhole

Oshiomhole yana tare da Tinubu

The Cable tace tsohon gwamnan na Edo ya yi wa Obi raddi ne bayan ya yi wata hira da CNN, inda yake bayanin yadda ake fama da rashin tsaro.

Oshiomhole ya taba rike shugabancin kungiyar kwadagon Najeriya ta Nigeria Labour Congress (NLC), wanda take yi wa Obi yakin zabe a 2023.

Oseloka H. Obaze wanda ya yi aiki da Obiano da Obi a matsayin sakataren gwamnati ya karyata Oshiomhole, yace Obi ya fara yakar Bakassi Boys.

Rabiu Kwankwaso ya ziyarci Minna

Kun ji labari Rabiu Kwankwaso mai neman mulki a NNPP ya karasa yawan bude ofisoshin NNPP a Neja da ya ziyara zuwa wajen manyan kasa.

Bisa al’ada, duk wanda ya je Minna, ya kan je har gida ya mika gaisuwa ga Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdusalam Abubakar

Asali: Legit.ng

Online view pixel