Gwamna Makinde Ya Tarbi Atiku, Okowa, Mambobin NWC Na PDP, Da Sauran Jiga-Jigai
- Jiga-jigan jam'iyyar PDP sun kai ziyara birnin Ibadan na jihar Oyo, ciki har da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar
- Atiku Abubakar zai yiwa wakilan jam'iyyar PDP na yankin Kudu maso Yamma jawabi a yayin wannan ziyara
- A watan nan ne jam'iyyun siyasan Najeriya za su fara tallata 'yan takara gadan-gadan gabanin zaben 2023
Jihar Oyo - The Nation ta ruwaito cewa, Gwamnan Seyi Makinde na jihar Oyo ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a gidan gwamnatin jihar dake Agodi, birnin Ibadan.
Atiku dira gidan gwamnatin na Oyo ne tare da abokin gaminsa a tafiyar 2023, Ifeanyi Okowa da misalin karfe 11:46 na safe.
Hadimin gwamnan jihar, Bayo Lawal ne ya tarbe su a filin jirgin sama na Ibadan, kamar yadda rahotanni suka bayyana, rahoton BluePrint.
Jim kadan bayan isowarsu gidan gwamnati, Makinde ya jagoranci jiga-jigan na PDP zuwa wani daki, inda suka yi wata ‘yar gajeruwar tattaunawa
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ganawar ta dauki tsawon mintuna 15 ne kacal tare da wasu mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam'iyyar.
Bayan kammala tattaunawar, gwamnan ya sanar da cewa tawagar Atiku za ta dunguma zuwa dakin taro na Theophilus Ogunlesi, daura da Asibitin Kwalejin Jami’ar Ibadan, inda Atiku zai yi jawabi ga wakilan PDP a Kudu maso Yamma.
Tawagar da ke tare da Atiku
Daga cikin 'yan tawagar sun hada da:
- Gwamna Aminu Tambuwal
- Sanata Dino Melaye
- Sanata Jumoke Akinjide
- Sanata Biodun Olujimi
- Tsohon Gwamna Ayodele Fayose
- Olusegun Mimiko
- Olagunsoye Oyinlola
- Zababben gwamnan Osun, Sanata Ademola Adeleke
- 'Yar takarar gwamnan Ogun Ladi Adebutu
- Dan takarar gwamnan jihar Legas Jide Adediran
- Eyitayo Jegrde
- Babangida Aliyu Muazu
- Cif Raymond Dokpesi
- Elder Wole Oyelese da dai sauransu
Zan Cire Najeriya Daga Kungurmin Duhu Idan Na Gaji Buhari, Inji Dan Takarar PDP Atiku
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin fidda Najeriya Najeriya daga kungurmin duhun da take ciki idan aka zabe shi a zaben 2023.
Ya bayyana haka ne yayin da yake magana a wani taron kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas (LCCI) ta 2022 da aka yi a Legas, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma shawarci 'yan Najeriya da cewa, kada su rudu da siyasar farfaganda da barbade a kafafen Facebook, Twitter da Instagram, inda yace hakan ba zai kare su da komai ba.
Asali: Legit.ng