2023: Dogara Da Babachir Sun Gana Da Kiristocin Arewa Don Kalubantar Gamin Tinubu Da Shettima
- Yakubu Dogara da Babachir David Lawal na ci gaba da tuntuba dangane da matsayinsu kan tikitin Musulmi da Musulmi da APC ke yi
- Jiga-jigan jam’iyyar mai mulki biyu sun gana da shugabannin kirista a jihohin arewa da FCT don nuna rashin yardarsu ga tikitin Tinubu/Shettima
- Tsohon kakakin majalisar wakilan ya ce za su ci gaba da fafutuka don ganin an yi adalci gabannin zaben na 2023
Manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Hon. Yakubu Dogara da Babachir David Lawal, suna ci gaba da nuna rashin gamsuwarsu a kan tikitin Musulmi da Musulmi, cewa za su ci gaba da fafutuka don ganin an yi adalci.
Dogara, wanda ya kasance tsohon kakakin majalisar wakilai, shine ya bayyana hakan bayan ganawarsu da shugabannin kiristoci daga jihohin arewa 19 da babbar birnin tarayya a ranar Talata.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ya kasance Musulmi shine dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2023, inda jam’iyyar ta sake zakulo tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima wanda shima Musulmi ne don ya zama abokin takararsa.
Dogara, wanda ya je shafinsa na Twitter a ranar Talata, 13 ga watan Satumba, ya ce sun gana da shugabannin kiriostocin arewa da birnin tarayya don yanke hukunci kan tsarin da Najeriya za ta bi wajen rungumar zaben 2023.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya rubuta a shafin nasa:
“#NigeriaDecides2023- Muna ci gaba da fafutukar neman adalci. A yau, mun yi ganawar shawarwari da shugabannin kirista daga jihohin arewa 19 da birnin tarayya kan turbar da ya kamata Najeriya ta hau a 2023.”
Akwai Aiki A gaba: Sanatan PDP Ya Bayyana Abun Da Zai Faru Idan Ayu Ya Yi Murabus
A wani labarin, Sanata mai wakiltan yankin Benue ta arewa maso yamma, Emmanuel Orker-Jev, ya ce jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na iya tsintar kanta a ‘manyan rikice-rikice’ idan har shugabanta na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Sanatan wanda ya kasance jigon PDP ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, yayin da ya bayyana a shirin gidan talbijin din Channels na Sunday Politics.
Ayu na ta fuskantar matsin lamba a yan watannin da suka gaba, inda aka nemi yayi murabus daga bangarori daban-daban, musamman a sansanin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng