Lawan, Abdulsalam Da IBB Sun Yi Wata Ganawa Cikin Sirri

Lawan, Abdulsalam Da IBB Sun Yi Wata Ganawa Cikin Sirri

  • Wasu manyan jiga-jigan APC sun ziyarci Abdulsalam Abubakar da Ibrahim Badamasi Babangida a ranar Asabar, 10 ga watan Satumba
  • Daga cikin bakin da suka ziyarci tsoffin shugabannin Najeriyan a gidajensu da ke Minna harda shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan
  • Lawan ya ce ya kai ziyarar gashin kansa ne don duba Abdulsalami wanda ke farfadowa daga rashin lafiya

Niger - Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya gana da tsoffin Shugabannin Najeriya na mulkin soja, Janar Abdulsalam Abubakar da Janar Ibrahim Badamasi Babangida a gidajensu da ke Minna.

Lawan ya kuma gana da tsoffin Shugabannin cikin sirri a ziyarar na ranar Asabar, 10 ga watan Satumba.

Mambobin APC
Lawan, Abdulsalam Da IBB Sun Yi Wata Ganawa Cikin Sirri Hoto: @DrAhmadLawan
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Lawan ya fara ziyartan gidan Janar Abdulsalam kafin ya karasa gidan Babangida.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wani Ɗan Takarar PDP Daga Jihar Arewa a Zaɓen 2023 Ya Rasu

Bayan ya saka labule da tsoffin Shugabannin biyu, Lawan ya fadawa manema labarai cewa ya kawo ziyarar ne saboda rawar ganin da suke takawa wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban majalisar dattawan ya kuma bayyana cewa ya zo Minna ne don gaishe da Abdulsalami wanda ke farfadowa daga rashin lafiya.

Jaridar The Sun ta nakalto Lawan yana cewa:

“A matsayinsa na shugabanmu kuma jigon kasa, Muna ganin cewa akwai bukatar mu kawo wannan ziyara a yau don jajanta masa da iyalinsa.
“Muna godiya ga Allah kan rayuwar iyayenmu kuma muna addu’a Allah ya basu lafiya gaba daya don su ci gaba da kyawawan aikinsu na tabbatar da ganin cewa Najeriya ta ci gaba a hade kuma yan Najeriya su ci gaba da zaman lafiya a tsakaninsu.”

Sai dai kuma shugaban majalisar dattawan ya ki cewa komai game da zaben 2023, inda yace lallai ya zo Minna ne don ra'ayin kansa ba wai ziyarar siyasa ba.

Kara karanta wannan

Katsina: Yadda Yarinya Mai Shekaru 13 Ta Haddace Qur'ani, Ta Rubuta shi da Hannunta

2023: Ɗan Takarar Gwamna a PDP Ya Roki Tsohon Sakataren Gwamnati Ya Fice APC

A wani labarin, mun ji cewa yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2023, ɗan takarar gwamnan Katsina a inuwar PDP, Sanata Yakubu Lasdo Ɗanmarke, ya ziyarci tsohon Sakataren gwamnatin jiha, Mustapha Inuwa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yayin wannan ziyara, Lado Ɗanmarke, ya roki tsohon SSG ya sauya sheka zuwa PDP domin su haɗa ƙarfi.

Mustapha Inuwa, wanda ya rasa tikitin APC a annun tsohon shugaban hukumar SEMDAN, Dr Diko Raɗɗa, ya karɓi baƙuncin Lado da tawgaarsa a Ofishinsa na Kamfe dake cikin birnin Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel