2023: Ba Dole Bane Takara Musulmi da Musulmi, Sheikh Ahmad Gumi

2023: Ba Dole Bane Takara Musulmi da Musulmi, Sheikh Ahmad Gumi

  • Sheikh Ahamd Gumi, fitaccen Malamin Musulunci, ya yi sharhi kan manyan yan takarar shugaban ƙasa uku
  • Shehin Malamin yace a halin da Najeriya ta tsinci kanta, tana bukatar kwararren ɗan siyasa ne da zai iya shawo kan lamarin
  • A cewar Gumi, takara Musulmi da Musulmi da APC ta tsayar ba tilas bane kuma bai shafi addini ba

Kaduna - Shahararren Malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dr Ahmad Gumi, yace takarar Musulmi da Musulmi na jam'iyyar APC ba wani abu bane domin ba shi da alaƙa da addini.

Dailytrust tace Shehin Malamin ya roki 'yan Najeriya su haɗa kansu wuri guda su yi watsi da siyasar Kabila ko Addini saboda dukkan jam'iyyun siyasa na da kalubale a gabansu.

Sheikh Ahmad Gumi da Masu Neman Gaje Buhari.
2023: Ba Dole Bane Takara Musulmi da Musulmi, Sheikh Ahmad Gumi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sheikh Gumi ya yi wannan tsokacin ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a gidansa dake garin Kaduna game da babban zaɓen 2023 da ke ƙara kusanto wa.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Rubuta Wasika Ta Musamman Ga Yan Najeriya, Ya Faɗi Zaɓi Biyu Da Ya Rage Wa Mutane a 2023

Da yake amsa wata tambaya kan kalaman ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinuhu, wanda ya yi ikirarin "Lokaci na ne na zama shugaban ƙasa," Gumi ya ayyana Tinubu da shugaba nagari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa, Gumi yace:

"Bai dace yace lokinsa ne ba, babu wata tambaya kan waɗannan kalaman amma kar kace lokaci na ne. Shugaba ne na gari kuma zai iya (shugabancin Najeriya)."
"Tikitin Musulmi da Musulmi ba dole bane, dukkan mu mun san cewa baki ɗaya 'yan siyasan nan kuri'u kawai suke nema, wannan takara ta musulmi da Musulmi ba ta shafi Addini ba."
"Ko zasu cimma nasara ko a'a, bana son shiga hurumin da ba nawa ba, amma akwai kalubale. A taƙaice zan iya cewa kowace jam'iyya na da nata ƙalubale, tikitin Musulmi da Musulmi zai zama tamkar gwaji ga saura."

Kara karanta wannan

Ni Da Yan Najeriya Na Jimamin Mutuwar Mahaifiyarka, Muna Maraba Da Hawanka Mulki: Buhari ga Sarkin Ingila

Peter Obi na da sauran aiki - Gumi

Game da ɗan takarar jam'iyyar LP, Peter Obi, Shehin Malamin yace da sauran aiki babba a gabansa, akwai bukatar ya faɗaɗa zuwa sauran sassan Najeriya.

Malam Ahmad Gumi ya ƙara da cewa ya kamata (Peter Obi) ya mamaye dukkan yankuna, bawai ya killace siyasarsa a shiyya ɗaya ta Najeriya ba, jaridar Punch ta ruwaito.

Wane ɗan takarar ya dace ya gaji Buhari?

Da yake tsokaci kan takarar Atiku a PDP, Gumi ya bayyana cewa duk da tsohon mataimakin shugaban ya nemi takara lokuta da dama, "Najeriya na bukatar kwararren ɗan siyasa."

"Bamu bukatar ɗan koyo ya zama shugaban ƙasa, halin da Najeriya ta wayi gari a ciki yau yana bukatar ɗan siyasa mai kwarewa da zai magance lamarin."

A wani labarin kuma Ana Gab da Fara Yakin Neman Zaɓe, Atiku da PDP Sun Gamu da Gagarumin Cikas a Jihar Gombe

Kara karanta wannan

2023: Hanya Ɗaya Da Zamu Kawo Karshen Rikicin Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar Ya Magantu

A jadawalin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) za'a fara yaƙin neman zaɓe na takarar shugaban kasa ranar 28 ga watan Satumba.

Yayin da kowace jam'iyya ke shirye-shiryen da ya dace, a jihar Gombe, PDP ta yi babban rashin jigonta a gundumar Bajoga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel