Yadda Mambobin APC 5,000 Suka Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Kwara

Yadda Mambobin APC 5,000 Suka Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Kwara

  • Jiga-jigan siyasa akalla 5,000 ne suka sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta PDP
  • Mabobin sun koka da rashin samun cikakkakiyar kulawa da karuwa a jam'iyyar ta APC a jihar ta Kwara
  • A cewarsu, sun yanke komawa PDP ne ganin halayen tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki

Jihar Kwara - An samu tsaiko a APC yayin da dubban mambobinta a Ilorin ta jihar Kwara suka bayyana sauya sheka zuwa PDP.

Jaridar Thisday ta ruwaito cewa mambobin na jam’iyyar APC wadanda aka ce ba su gaza 5,000 ba sun saki jam'iyyar su Buhari kuma mai mulki a jihar zuwa ta adawa.

An tattaro cewa, wadannan jiga-jigai na APC da suka hakura suka koma PDP sun fito ne daga unguwanni da kananan hukumomin jihar Kwara da suka hada da Ilorin ta Yamma da kuma karamar hukumar Asa.

Kara karanta wannan

Ta karewa Tinubu, jam'iyyar PDP ta kwace ofishin kamfen din Buhari a Katsina

Haka kuma, da yawansu sun fito ne daga unguwanni irinsu Ajikobi, Ubandawaki, Ogidi, Adewole, Badari da dai sauransu a karamar hukumar Ilorin ta Yamma.

Jiga-jigan APC sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Kwara
Yadda Mambobin APC 5,000 Suka Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Kwara | Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, wasu daga cikinsu sun fito ne daga yankuna biyar na gundumar Laduba da suka hada da, Sapati, Abayawo, Budo-Ago da Ago-Oja, duk dai a karamar hukumar ta Asa ta jihar.

Rahoton ya ce, sun zo a a karkashin jagorancin Toyin Abdul, Olohuntoyin Rahmeen, Injiniya Yinka Yusuf da kuma wata tawaga ta ‘yan kabilar Ibo a garin Baboko.

Dalilin sauya shekarsu daga APC zuwa PDP

Da suke bayani, sun ce amince cewa sun yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC saboda rashin tabuka komai na gwamnatin jihar.

Sun kuma yi korafi da rashin gogewar aiki daga gwamnatin APC wajen samar da shugabanci mai kyau ga al’ummar jihar.

Kara karanta wannan

ASUU: Wasu Daliban Jami’a Sun Hada-kai, Sun Yi Karar Buhari da Ministoci a kotu

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, sun ce sun yanke shawarar ficewa daga APC ne domin marawa gogaggun shugabannin PDP da tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki baya.

Shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Baboko, Moshood Yakub ya karbe su hannu biyu, ya kuma nuna musu cewa, PDP na tare dasu a fafutukar da take na karbe mulki a Najeriya.

Jam’iyyar PDP Ta Karbe Ofisoshin Yakin Neman Zaben Buhari Na Katsina

A wani labarib, jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa, reshenta a jihar Katsina ya karbe ofisoshin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar.

Shugaban jam'iyyar ne na kasa, Iyorchia Ayu ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Ayu ya samu wakilicin hadiminsa a fannin yada labarai, Yusuf A. Dingyadi a jihar Katsina, inda yace tuni jijiyoyin PDP suka mamaye sassa daban-daban na mahaifar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

An Kai Korafi Zuwa Hedikwata, Ana Zargin Shugabannin APC da Satar Milyoyin Kudi

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.