Takarar Kujerar Shugabancin Kasa Ta Jawo An Tona Silar Arzikin Bola Tinubu a Duniya
- Dele Alake ya yi karin haske a kan yadda Bola Ahmed Tinubu ya samu dukiyar da kowa yake surutu a kan ta
- Darektan dabarun sadarwa na kwamitin yakin neman zaben APC yace Bola Tinubu ya dade da yin kudi
- ‘Dan siyasar yace shekaru fiye da 30 da suka wuce ‘dan takaran na APC ya yi arziki da saida hannun jari
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Darektan dabarun sadarwa na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Dele Alake ya tabo batun dukiyar Bola Ahmed Tinubu.
A karshen makon jiya aka yi hira da Dele Alake a gidan talabijin na Channels TV, ya bayyana cewa Bola Tinubu ya dade da samun dukiya a Duniya.
Alake ya tattauna batun takarar shugaban kasa da Bola Tinubu yake yi a zaben 2023, ya kuma wanke shi daga zargi a kan maganar silar arzikinsa.
Darektan na kamfe yace ‘dan takaran na su ba talaka ba ne tun a shekarar 1992 da ya fito takarar kujerar Sanata, yace ko a lokacin Tinubu ya yi kudi.
Tinubu ba a siyasa ya yi kudi ba
“Na san shi yana kashe kudi tun kafin ya samu kujerar siyasa. A shekarar 1991 ya shiga siyasa, ya yi takarar Sanata – kuma ya yi nasara.”
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Mutane da-dama sun san cewa shiga zabe a Najeriya ba wasa ba ne. Yara ba su iya tsayawa takara. Har kuma ayi batun zaben Sanata.”
“Dole yana da hanyar samunsa. Asali ma tun kafin nan, yana taimakawa kungiyoyin siyasa da gudumuwa, kafin ya shiga takarar majalisa.”
“A 1992, shi ya samu kuri’un da suka fi kowa yawa a zaben majalisar dattawa, ya zama Sanata.”
“Da aka zo shekarar 1993, muka fara gwagwarmayar June 12, yana cikin mutanen Yar’Adua’s – PF – a cikin jam’iyyar SDP, suke bada kudi.”
- Dele Alake
Harkar saida hannun jari
Jaridar The Cable da ta bibiyi wannan hira da aka yi a ranar Lahadi, ta rahoto Alake yana cewa masu maganar ina Tinubu ya samu dukiya, makiyansa ne.
Alake yace tun a lokacin da Tinubu yana aiki a kamfanonin ketare, ya shiga harkar saye da saida hannun jari, sannan ya rika cinikin kudin kasashen waje.
“Ya yi ta sayen hannun jari da sauransu. Ni ba masanin tattalin arziki ba ne, saboda haka ba zan san kan su ba. ya rika sayen hannu jari a kamfanoni, ya samu kudi.”
- Dele Alake
Za ayi wa Atiku ritayar siyasa
Dazu an ji labari Sanata Kashim Shettima yace babu ta yadda za a hada Atiku Abubakar da Bola Tinubu, domin Atiku bai taimaki kowa a mulki ba
Shettima ya jefawa ‘dan takaran na PDP kalubale, yace a shekaru takwas da suka yi, Atiku ba zai iya nuna ayyuka uku da ya kawowa yankin Arewa ba.
Asali: Legit.ng