2023: Ana Gabanin Fara Kamfe, Kwankwaso Ya Ja-kunnen Tinubu, Atiku da Peter Obi

2023: Ana Gabanin Fara Kamfe, Kwankwaso Ya Ja-kunnen Tinubu, Atiku da Peter Obi

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara zuwa Adamawa, a nan ma ya bude sakatariyar jam’iyyar NNPP
  • Sanata Kwankwaso ya yi kira ga babbar murya ga masu yin takarar shugaban kasa da su nuna dattakunsu
  • ‘Dan siyasar ya yi magana game da hadarin raba kan jama’a, ya kuma ce har yanzu bai fara yin kamfe ba

Adamawa - Rabiu Musa Kwankwaso wanda yake harin zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar NNPP ya kai ziyara zuwa jihar Adamawa.

Rahoton Sahelian Times ya tabbatar mana da cewa a Adamawa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga masu neman mulkin kasar nan a 2023.

Kiran da ‘dan takaran ya yi shi ne a guji yin kalaman da za su tada hankali, ya bukaci masu neman mulki su maida hankali ga abubuwan da ke gabansu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Rahoton yace tsohon Gwamnan na Kano kuma ‘dan takaran shugaban kasa na NNPP ya gargadi abokan aikinsa ‘yan siyasa a kan yin kalaman kiyayya.

A nuna halin dattaku - Kwankwaso

Da yake magana a sabuwar sakatariyar NNPP da ke garin Yola, Rabiu Kwankwaso yace dole ne ayi siyasa da kamala da dattaku domin kai ga nasara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Manyan masu neman mulki a zabe mai zuwa su ne: Bola Tinubu, Peter Obi da Atiku Abubakar, wanda a mahaifarsa Kwankwaso ya yi wannan magana.

Kwankwaso
Kwankwaso a garin Mubi Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Kafin nan an ji Peter Obi ya yi kira ga babbar murya ga mabiya su guji bata kowa. A jiya ne wani jigo a APC makamancin wannan kira ga ‘yan siyasa.

Ban fara kamfe ba - Kwankwaso

Jaridar People Gazette ta rahoto ‘dan siyasar yana cewa bai ziyarci jihar ta Adamawa domin ya yi kamfe ba, yace lokacin yakin neman zabe bai yi ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Jigon Jam’iyya Ya Fadawa Peter Obi Sirri 5 Na Lashe Zaben Shugaban Kasa

Dinbin mutane sun samu halartar wannan biki na kaddamar da ofishin NNPP a Yola. Bayan nan ya kai gaisuwa wajen Sarkin Mubi, Abubakar Adamu

Sanata Kwankwaso ya zagaye wasu jihohin kasar nan yana bude ofisoshin jam’iyyar NNPP.

Jam’iyyar adawar mai alamar kayan dadi da aka farfado da ita ta bude ofisoshinta a Kaduna, Kano, Borno, Adamawa, Neja, Kogi, Gombe da Bauchi.

NNPP za ta ci zabe a Kano, Kasa

Mun tuntubi wani Hadimi da ke taimakawa Rabiu Kwankwaso bayan NNPP ta maye gurbin Ibrahim Shekarau, ya nuna mana suna hangen nasara.

Kun ji labari Saifullahi Hassan ya nuna ficewar Ibrahim Shekarau ba za ta hana su nasara a Kano ba, bugu da kari, yace suna fatan cin babban zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng