2023: Duk Wata Boye-Boye Ta Zo Karshe, An Gano Dan Takarar Da Obasanjo Zai Mara Wa Baya
- Wasu yan PDP sun tabbatar da cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo zai goyi bayan Atiku Abubakar a 2023
- Mai magana da yawun kamfen din Atiku, Charles Aniagwu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba 7 ga watan Satumba
- Aniagwu ya ce bayan aikin da ya yi da Atiku daga 1999 zuwa 2007, Obasanjo ya san iya jagoranci na tsohon mataimakin shugaban kasar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Asaba, Delta - Kakakin kamfen din Atiku Abubakar, Charles Aniagwu ya jadada cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo zai goyi bayan mai gidansa a zaben 2023.
Da ya ke magana da yan jarida a Asaba a ranar Laraba, 7 ga watan Satumba, Aniagwu ya ce Obasanjo ya san kwarewa ca cancantar Atiku saboda ya taka muhimmin rawa wurin daidaita tattalin arzikin Najeriya daga 1999 zuwa 2007, PM News ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce duk da cewa yan siyasan biyu sun samu sabani a wasu bangarorin, Obasanjo ya goyi bayan takarar Atiku a 2019, ya kara da cewa babu abin da ya canja daga wancan lokacin zuwa yanzu.
Aniagwu ya ce:
"Ina son bada misali da 2019, tsohon shugaba Obasanjo ya goyi bayan Atiku. Tamkar ma dai Atiku dan takarar Obasanjo ne, idan ya goyi bayansa, bana tunanin wani abu ya canja tsakanin 2019 zuwa yanzu.
"Kuma, tsohon shugaban kasa Obasanjo, mutum ne da muke girmamawa sosai.
"Mun yi imanin cewa Obasanjo mutum ne da ke yi wa kasar nan fatan alheri, ya nuna hakan a hanyoyi daban-daban. Ya ga basira a tattare da Atiku a 1999, shi yasa ya zabe shi matsayin abokin takara."
Olusegun Obasanjo Ya Ce Bangaren Tinubu Sun Masa 'Sharri'
A wani rahoton, Olusegun Obasanjo ya gargadi wasu magoya bayan Asiwaju Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Daily Trust ta rahoto.
Tinubu da wasu jiga-jigan APC sun ziyarci Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta, babban binrin Jihar Ogun, a ranar Laraba.
Cikin wadanda suka yi wa Tinubu rakiya akwai tsaffin gwamnonin jihar Ogun, Olusegun Osoba da Otunba Gbenga Daniel, dan kasuwa kuma tsohon shugaban riko na APC, Cif Bisi Akande da Kakakin Majalisa, Femi Gbajabiamila.
Obasanjo da Tinubu dukkansu ba su yi magana da manema labarai ba bayan taron.
Asali: Legit.ng