Ku Daina Yaudarar Mutane: Jigon APC Yana Neman Cirewa Tinubu Zani a Kasuwa

Ku Daina Yaudarar Mutane: Jigon APC Yana Neman Cirewa Tinubu Zani a Kasuwa

  • Mista Tunde Bank-Anthony ya zargi magoya bayan Bola Tinubu da karya da nufin tallata gwaninsu a 2023
  • ‘Dan siyasar ya soki masu cewa Tinubu ya gina Legas, alhali tun kafin ya zama Gwamna a 1999, jihar tayi nisa
  • Ana zargin wasu da dunkule ayyukan Babatunde Fashola da Akinwumi Ambode a matsayin nasarorin Tinubu

Lagos - Tunde Bank-Anthony wanda jagora ne a tafiyar APC a jihar Legas, ya ja-kunnen magoya bayan Bola Ahmed Tinubu a game da yaudarar al’umma.

Tunde Bank-Anthony ya yi hira da tashar Channels TV, a nan ya shaida cewa magoya bayan Bola Tinubu suna yin karya domin ‘dan takaransu ya karbu.

‘Dan siyasar yace kafin Bola Tinubu ya zama Gwamnan Legas a 1999, sauran shugabanni da aka yi a jihar sun yi fiye da abin da ya yi a shekaru takwas.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya yi Maganar Dukiyarsa, Ya Nesanta Kan Shi Daga Arzikin Da Ake Jingina Masa

Kakakin na kungiyar Concerned Lagosians ta ‘ya ‘yan APC yake cewa ayyukan da Babatunde Fashola ya yi, sun sha gaban na uban gidansa watau Tinubu.

Mai magana da yawun ‘yan kungiyar ta Concerned Lagosians ya yi kira ga mutanen Tinubu su nemi wani abin da za su yi kamfe, ba su ci da gumin wasu ba.

A cewarsa, magoya bayan ‘dan takaran shugaban kasar suna hada nasarorin Fashola, Akinwumi Ambode, Babajide Sanwo-Olu duk a matsayin aikin Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asiwaju
'Dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Bank-Anthony ya yi wannan bayani a shirin Sunrise Daily na ranar Laraba, 7 ga watan Satumba 2022, The Cable ta kawo labarin.

Ba Tinubu ya tada Legas ba - Kungiya

“’Dan takaranmu (Tinubu) yana kamfen da Legas, sai a dauka cewa a cikin shekaru 100 da suka wuce, jihar ba ta taba samun irinsa ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Dole mu ‘Yan Legas mu fayyace komai. Shekara ta kusan 60 a Duniya, a cikin birnin Legas na tashi, babu hanyar da babu titi a lokacin.
Amma matsalar ita ce, siyasar da ake yi yanzu tana damunmu. Batun cewa ‘dan takaran jam’iyyarmu ya gina Legas, ba gaskiya ba ne.
Tun can Legas take Legas. Idan ka kira birnin New York, birnin Faris, ko birnin Landan, dole za ka kira Legas.
Shi Tinubun ne ya gina makarantar da ya halarta lokacinsa? Shi ya gina asibitin da aka haife shi?

- Tunde Bank-Anthony

Rikici a gidan PDP

Shugaban jam’iyya na kasa, Iyorchia Ayu, Shugaban BOT, Walid Jibrin, Namadi Sambo, Atiku Abubakar da shugabannin PDP sun yi wani taro a Abuja.

An ji labari Gwamna Nyesom Wike da sauran ‘yan tawagarsa sun kauracewa wannan zama da aka yi, Gwamnoni akalla takwas suka gujewa zaman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng