An Girke Jami’an Tsaro Carko-Carko a Sakateriyar APC, Tinubu da Shettima Za Su Kai Ziyara
- An girke jami'an tsaro a sakateriyar APC yayin da ake sa ran Tinubu da Shettima za su kai ziyara
- Tinubu da Shettima za su kai ziyarar ne ta farko tun bayan kammala zaben fidda gwani na jam'iyyar
- A ranar 28 ga watan nan ne za a fara gangamin kamfen din 'yan takarar shugaban kasa, kowacce jam'iyya na shiri
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima za su kai ziyara sakateriyar jam'iyyar APC a yau Laraba, 7 ga watan Satumba, Punch ta ruwaito.
Rahoton da muke samu ya ce, tuni an girke jami'an tsaro ta kowacce kofa da sakon sakateriyar a shirye-shiryen karbar jiga-jigan na APC.
An ga motocin sintiri da dama a zagaye da sakateriyar manyan jami’ai dake kai komo a zagayenta.
An ce Tinubu da Shettima za su halarci wata ganawar wucin gadi ne da kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na kasa a sakatariyar da misalin karfe 10:00 na safe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan watanni uku da Tinubu ya dage kai ziyarar farko ga sakatariyar bayan lashe zaben fidda gwanin shugaban kasa da aka a APC.
Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga jam’iyyar APC, majiya ta ce ganawar za ta ba da damar tattaunawa kan shirin kamfen din Tinubu da kuma sake fasalin tsarin shi kansa kamfen din da za a fara a ranar 28 ga watan nan.
Hakazalika, majiyar ta kuma kara da cewam za a takaita adadin wadanda za su shiga cikin sakatariyar domin rage cunkoson jama’a da kuma wasu dalilai na tsaro.
Ana sa ran Tinubu da Shettima su yiwa manema labarai bayani a sakateriyar jam’iyyar ta APC bayan kammala ganawar.
Jerin 'Yan Siyasan Najeriya da Kungiyoyin Dake Yiwa Tinubu Gangamin 2023
A wani labarin, babu shakka, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ko kwararre ne wajen kitsa tafiyar siyasa tare da zabo wadanda suka cancanta a tafiyarsa.
Ya zuwa yanzu dai Tinubu ya yi cudanya da jiga-jigan siyasa a ciki da wajen Najeriya yayin da yake ci gaba da tallata aniyarsa ta neman gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.
A yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, tsohon gwamnan na Legas sananne ne wajen kitsawa da daura wasu fitattun 'yan siyasa a kujeru daban-daban, musamman gwamnoni.
Asali: Legit.ng