2023: Muhimman Abubuwa 5 da Ka Iya Shafar Nasarar Tinubu, Atiku da Obi a Zabe Mai Gabatowa
- CDD ta bayyana manyan kalubalen da 'yan takarar shugabancin kasa 3 a Najeriya ka iya fuskanta a zaben shekara mai zuwa
- Rashin tsaron arewa maso yamma na iya hana masu kada kuri'u fitowa wanda hakan na iya canza alkalumman kuri'un Bola Tinubu
- A kudu kuwa, 'yan awaren kasar nan na iya hana masu kada kuri'un bayyana ranar zabe wanda hakan zai shafi Peter Obi da Atiku
- Sai dai cibiyar ta ja kunne kan rashin tsaro, yada labaran bogi, siyasar kudi, addini da kabilanci na iya sauya alkalumman zabe a shekarar 2023
Matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma na iya taka rawar gani wurin rage kuri'un da 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, zai iya samu a zaben 2023.
Sabon rahoton da Cibiyar Damokaradiyya da Cigaba ta sanar da hakana a ranar Talata, jaridar Punch ta rahoto.
Kungiyar tace 'yan awaren yankin kudu maso gabas zasu iya rage yawan masu kafda kuri'u, wanda hakan na iya zama barazana ga 'dan takarar Labour Party, Peter Obi ko kuma 'dan takarar PDP, Atiku Abubakar.
CDD ta yi wannan bayanin ne a rahoto mai suna ‘Nigeria’s presidential polls: A SWOT Analysis’ da ta saki a Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kungiyar ta jan kunne kan:
Rashin tsaro
Yada labaran bogi
Siyasar kudi
Addini da
Kabilanci na iya sauya alkalumman zabe a shekarar 2023.
Rahoton da daraktan CDD, Idayat Hassan ta saka hannu, tace hukumar zabe mai zaman kanta za ta bukaci jami'an tsaro da ma'aikatan zabe 1.5 miliyan domin samun yin zaben cike da kwanciyar hankali.
Rahoto yace:
"Yayin da kamfen ke tahowa a makonni masu zuwa, manyan matsalolin gwamnati kamar rashin tsaro zai zama abin duba ga manyan 'yan takarar kasar nan.
"Rahoton yace yankin arewa maso yamma shi ne wurin da rashin tsaron rayuka da kadarori zai taka rawar gani wurin rage kuri'un Tinubu.
“A lokaci daya kuma, 'yan awaren kudu maso gabas na iya rage yawan masu fitowa kada kuri'u, wanda na iya rage yawan kuri'un Peter Obi da Atiku Abubakar."
Kamar yadda rahoton ya bayyana, illar banbancin addini, kabila da siyasar kudi na iya hana zaben gaskiya kuma cikin lumana idan ba a shawo kan hakan ba.
2023: FBI da EFCC Sun Bankado Sirrikan Mashahuriya Dukiyar Bola Tinubu
A wani labari na daban, Joe Igbokwe, makusancin Bola Ahmed Tinubu, ya bankado abinda Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC yace gane da tsohon gwamnan jihar Legas yayin da yake shugabancin hukumar.
Kamar yadda wallafar da Igbokwe yayi a Facebook ta bayyana, Ribadu ya bayyana cewa daya daga cikin jihohin da ya sanyawa ido yayin da yake EFCC shi ne jihar Legas.
A wallafar Igbokwe, Ribadu ya bayyana cewa ya fara bincike kan zargin almundahanar kudade a jihar yayin da Tinubu yake gwamnan Legas.
Asali: Legit.ng