Tikitin Musulmi Da Musulmi: Za A Maye Gurbin Shettima Cikin Sati 2? Sabon Bayani Ya Fito Daga APC

Tikitin Musulmi Da Musulmi: Za A Maye Gurbin Shettima Cikin Sati 2? Sabon Bayani Ya Fito Daga APC

  • Tikitin Musulmi Da Musulmi: Shin Za A Maye Gurbin Shettima Cikin Sati 2? Sabon Bayani Ya Fito Daga Yan APC Na Arewa
  • An yi kiraye-kiraye ga jam'iyyar APC ta maye gurbin Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasarta
  • A wani sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, 5 ga watan Satumba, masu da ruwa da tsaki daga APC na arewa maso gabas da arewa ta tsakiya sun kallubalanci zabin Shettima

Masu ruwa da tsakin na jam'iyyar APC sun shawarci jam'iyyar ta maye gurbin Shettima kafin ranar Talata, 20 ga watan Satumba, lokacin da INEC za ta fitar da jerin sunayen yan takarar zaben 2023

Hadakar masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC daga arewa maso gabas da arewa ta tsakiya sun shawarci shugabannin jam'iyyar ta sake duba zabin da aka yi wa Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa gabanin 2023.

Tinubu, jonathan
Tikitin Musulmi Da Musulmi: Za A Maye Gurbin Shettima Cikin Sati 2? Sabon Bayani Ya Fito Daga APC. Hoto: (Joe Igbokwe)
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mambobin na APC sun kuma bukaci jam'iyyar ta janye nadin da aka yi wa Gwamna Simon Lalong a matsayin direkta janar na kungiyar yakin neman zabenta, The Punch ta rahoto.

A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, 5 ga watan Satumba, sakatare janar na masu ruwa da tsakin, Dauda Yakubu, ya ce tikitin musulmi da musulmi da APC ta yi na janyo rashin jituwa tsakanin mambobinta.

Yakubu ya ce APC tana da dama har zuwa ranar 20 ga watan Satumba, lokacin da INEC za ta fitar da sunayen yan takarar zaben 2023 na karshe, ta duba batun zargin wariya da kiristoci suka ce ana musu.

A cewarsa, zaben Kashim Shettima da Asiwaju Bola Tinubu ya yi a matsayin abokin takararsa nuna rashin kishi ne da mutunta sauran addinai a Njeriya.

Ya ce:

"Shugabannin hadakar ta arewa maso gabas da arewa ta tsakiya na masu ruwa ta APC tana taro don daukan mataki da zai iya shafar sakamakon zaben shugaban kasa da ke tafe.
"Ba boyayyen lamari bane cewa tikitin musulmi da musulmi da jam'iyyar ta yi ya janyo guna-guni a jam'iyyar, musamman arewa ta gabas da arewa ta tsakiya a kasar.
"Zabin Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC ya saka alamar tambaya kan matsayar jam'iyyarmu na girmama dukkan kabilai da addinai a kasar.
"Hakan na zuwa ne bayan jam'iyyar ta zabi da yi watsi da mambobin jam'iyyar na arewa maso gabas da arewa ta tsakiya kiristoci da suka cancanta a zabe su a matsayin yan takarar mataimakin shugaban kasa ..."

2023: Ƙungiyar Mayu Da Matsafa Ta Najeriya Ta Yi Magana Mai Ƙarfi Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC

A wani rahoton, Cif Okhue, kakakin kungiyar Fararen Mayu da Matsafa ta Najeriya (WITZAM), ya ce babu wani matsala don jam'iyyar APC ta tsayar da musulmi biyu a takarar shugaban kasa da mataimaki.

Ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke bayyana cewa nan bada dadewa ba kungiyar za ta hango wanda zai zama shugaban kasa a 2023, Independent ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel