Gwamna Wike Ya Tona Abin da Ya Sa Buhari ya Zarce, Aka Doke Atiku a zaben 2019

Gwamna Wike Ya Tona Abin da Ya Sa Buhari ya Zarce, Aka Doke Atiku a zaben 2019

  • Nyesom Wike yace sai da wasu jagorori a PDP suka zo wajen shi domin taimakawa jam’iyyar APC a zaben 2019
  • Gwamnan na Ribas yake cewa bai yi na’am da wannan ba, ya dage cewa sai PDP tayi nasara a zaben da ya wuce
  • Wike ya kawo wannan labari ne domin ya nuna ba zai goyi bayan kowa a 2023 ba, sai wanda zai taimaki jihar Ribas

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas yace ba komai ne ya kara taimakawa Muhammadu Buhari a zaben 2019 illa gudumuwar wasu ‘ya 'yan PDP.

A yau Talata, 6 ga watan Satumba 2022, Daily Trust ta rahoto Nyesom Wike yana cewa akwai jagororin PDP da suka ba jam’iyyar APC gudumuwa a 2019.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Zan Lallasa Tare da Mitsike Kananan Yara, Gwamna Wike

Mai girma Nyesom Wike yake cewa wasu kusoshi da ake ji da su a jam’iyyar adawa ta PDP sun zauna da shi domin ya ba APC hadin-kai a zaben da ya wuce.

A cewar Gwamnan na Ribas, bai amince da wannan magana da aka zo masa da ita a lokacin ba. Duk da haka, Muhammadu Buhari ya yi galaba a kan PDP.

Har ‘dan siyasar ya gama bayaninsa, bai kama sunayen manyan PDP da suka zo wajensa da nufin a ba APC hadin-kai wajen samun kuri’u a jiharsa ba.

Channels TV ta haska taron, aka ji tsohon Ministan yana bayanin yadda a cewarsa gwamnatin Muhammadu Buhari ta yaki mutanen Ribas, amma suka tsira.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna Wike
Gwamnan Ribas, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Asali: Facebook

Jawabin Gwamna Wike

“Lokacin da za su shiga yarjejeniya da shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019, sun zo wajena, na fada masu: ‘Sam; babu sulhu, dole PDP ta ci zabe.

Kara karanta wannan

Sulhu a Jam’iyyar PDP Ya Gagara, Wike da Gwamnoni Sun Yi Kus-Kus a Landan

Nace a’a.' Wannan ya sa Buhari ya ci wannan zabe. Wadanda suka tabbatar PDP ba ta kai labari a 2015 ba, suka rusa PDP, ina gani suna bude baki yau.

- Nyesom Wike

A jawabinsa, Wike yace babu ruwansa da ‘dan takaran da bai da niyyar kawo cigaba a Riba.

A karshe, ya yi martani ga abokan fadansa a jam’iyyar hamayya ta PDP, yace wasu suna kiransu yara duk da wadannan mutane sun sauya-sheka a siyasa.

An karasa aikin Jami'a a Etche

Mista Wike ya yi wannan bayani ne a ranar Talatar nan a lokacin bikin kaddamar da wani sashe na jami’ar jihar Ribas da gwamnatinsa ta gina a garin Etce.

Mai girma gwamnan ya kawo wannan labari domin ya nuna cewa babu wanda ya isa ya tursasa shi wajen goyon bayan abin da ba zai taimaki jihar Ribas ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng