Dino Melaye da Fani-Kayode Sun Dauki Zafi, Sun Yi Wa Junansu Kaca-Kaca a Idon Duniya
- Femi Fani-Kayode ya dauko wata magana da Dino Melaye ya yi a kan zaman Iyorchia Ayu shugaban PDP na kasa
- Cif Femi Fani-Kayode ya bada shawarar a damke Dino Melaye saboda kalamansa a game da Gwamnonin jihohinsu
- Wannan ya jawo Sanata Melaye ya maida martani, daga nan sai tsohon Sanatan ya maida masa martani a shafinsa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Dino Melaye wanda ke magana da yawun bakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, ya yi arangama da Femi Fani-Kayode a Twitter.
Legit.ng Hausa ta lura Femi Fani-Kayode ya yi magana a shafinsa na sada zumunta, yana kira ga gwamnatin tarayya da jami’an tsaro su cafke Dino Melaye.
Hakan na zuwa ne bayan an rahoto Sanata Dino Melaye yana mai bayanin yadda gwamnoni suka kashe kudi wajen zaman Iyorchia Ayu shugaban PDP.
A cewar tsohon Ministan na harkokin jirgin saman, ya kamata ayi ram da Melaye tun da ya tona gwamnonin jihohi da rawar da suka wajen kawo Dr. Ayu.
Baya ga haka Fani-Kayode ya bukaci a hana Atiku Abubakar tsayawa takarar shugaba kasa.
Martanin Sanata Dino Melaye
Amma da Melaye ya tashi maida masa martani, yace ba za a iya fahimtar abin da Fani-Kayode yake nufi ba, yace jagoran na APC ya saba fadan soki-burutsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daily Trust ta rahoto tsohon ‘dan majalisar yace babu dalilin da Femi Fani-Kayode zai kinkimo tsohuwar hirar da aka yi da shi, ya na kafa hujja da ita a yau.
Kakakin na kwamitin yakin neman zaben Atiku yace abin da ya dace shi ne ayi watsi da FFK, amma zai yi karin haske saboda ya warware zare da abawa.
Kai kaska ne - FFK ga Dino
Da ya tashi yin raddi a Twitter, Fani-Kayode yace Melaye ba komai ba ne sai kaska a siyasa.
“Me mutum zai ce a game da kaskan da ya bi Nasir El Rufai na shekaru, daga nan ya koma bin Bukola Saraki, sai ya bi Yahaya Bello…
Daga nan ya bi Nyesom Wike, yanzu ya tare a wajen Atiku, ya cigaba da nuna masifar kwadayi."
- Femi Fani-Kayode
Bayan nan tsohon Sanatan na yammacin Kogi ya cigaba da habaici da maganganu a shafinsa na Twitter, har da dauko bidiyo domin cin mutuncin Fani-Kayode.
Wike ya koma Landan
A baya an ji labari Gwamnan jihar Ribas watau Nyesom Wike ya zauna da wasu gwamnoni domin cigaba tattaunawa daga inda aka tsaya a kan rikicin PDP.
Ana tunanin Bola Tinubu zai hadu da Gwamnonin na PDP a kasar waje, wanda hakan barazana ce ga takarar Atiku Abubakar na zama shugaban Najeriya.
Asali: Legit.ng