EFCC Ta Tafi Kotu, Tana Zargin Kakakin Majalisar Ogun, Olakunle Oluomo Da Sace Kudade

EFCC Ta Tafi Kotu, Tana Zargin Kakakin Majalisar Ogun, Olakunle Oluomo Da Sace Kudade

  • Hukumar EFCC na tuhumar kakakin majalisar dokokin jihar Ogun da laifin sace wasu kudade a jiharsa
  • A makon da ya gabata ne EFCC ta kame Olakunle Oluomo a jihar Legas yayin da yake kokarin hawa wani jirgi
  • EFCC ta bayyana cewa, tana da shaidun da za ta gurfanar domin tabbatar da laifin dan siyasan da kuma wasu mutum uku

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abeokuta, jihar Ogun - Jim kadan bayan kame shi kakakin majalisar dokokin jihar Ogun Olakunle Oluomo, hukumar EFCC ta shigar da wasu tuhume-tuhume 11 kansa tare da wasu mutum uku.

EFCC na zargin kakakin ne da hada baki tare da karkatar da wasu kudade, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Rotimi Oyedepo dake jagorantar sashen sa ido kan shari’a na EFFC a Legas ne ya shigar da karar a babbar kotun tarayya dake Abeokuta, jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Mutane 9 Sun Mutu, 10 Sun Jikkata A Mumman Hadarin Mota A Abuja

Olakunle Oluomo zai fusanci fushin EFCC
Bayan tsige kakakin majalisar Ogun, EFCC sun maka shi a kotu bisa zarge-zarge 11 | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Gidan talabijin din ya ce ya samu kwafin takardar tuhumar da aka shigar kan kakakin na Ogun a ranar 1 ga Satumba, 2022.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran mutum uku da ake tuhumarsa tare da su sun hada da Oladayo Samuel, Adeyemo Adedeji Taiwo da Adeyanju Nimota Amoke.

Tuhume-tuhumen da EFCC ke musu

Daya daga cikin tuhume-tuhumen na zargin dan siyasar da hada baki wajen sace kudaden da suka kai N2,475,000,000,000 a 2019.

A bangare guda, EFCC ta ce tana da shaidu akalla 10 da za su ba da shaida da kuma kawo takardun da ke nuna sun aikata laifukan.

Shaidun da EFCC za ta gabatar su ne:

  1. Adamu Usman Yusuf
  2. Otitoju Moses Kolawale
  3. Yazid Ahmad Bawa
  4. Anyanwu Bright
  5. Adekunbi Mojibola
  6. Munkaila Huzaifa
  7. Idowu Oluseyi Olarenwaju

Sauran wadanda za su yiwa EFCC shaida sun hada da wakilan Ashkash Nigeria Limited, Obasanjo Holdings Limited (manajojin gidajen mai na NNPC) da kuma na Bankin Gateway.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

Wata majiya ta ce, EFCC za ta bibiyi batun karar a Abeokuta a cikin makon nan.

A baya dai an ba da belinsa baya, kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito.

Hukumar EFCC Ta Kwmaushe Kakakin Majalisar Dokokin Ogun Olakunle Oluomo

A wani labarin, hukumar yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta kwamushe kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo, Channels Tv ta ruwaito.

An cafke kakakin ne da misalin karfe 9 na safiyar yau Alhamis, 1 ga watan Satumba a filin jirgin saman Murtala Mohammed dake birnin Legas.

Majiyoyi sun shaida cewa, jami’an hukumar ta EFCC sun tafi dashi ne domin titsiye shi tambayoyin da suka shafi laifin karkatar da kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.