2023: Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Bayyana 'Yan Takara Da Ya Kamata Matasan Najeriya Su Zaba

2023: Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Bayyana 'Yan Takara Da Ya Kamata Matasan Najeriya Su Zaba

  • Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya shawarci matasan Najeriya gabannin babban zaben 2023
  • Jonathan ya bukaci matasa da su zabi shugabanni da za su karfafa zaman lafiya da hadin kan kasar
  • Ya ce yan siyasa masu haddasa rikicin kabilanci basu cancanci a zabe su ba

Imo - Gabannin babban zaben 2023, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya shawarci matasan Najeriya da su zabi wadanda za su karfafa zaman lafiya da hadin kan kasar.

Tsohon Shugaban Najeriyan ya bukaci matasa da kada su zabi wadanda za su tunzura rikicin kabilanci da addini a fadin kasar da kuma kawo tsaiko a ci gaban kasar.

Goodluck Jonathan
2023: Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Bayyana 'Yan Takara Da Ya Kamata Matasan Najeriya Su Zaba Hoto: guardian.ng
Asali: Depositphotos

Jonathan ya bayar da wannan shawarar be a ranar Asabar, 3 ga watan Satumba, Owerri, baban birnin jihar Imo, New Telegraph ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban CAN ya magantu kan abin da ya kamata fastoci su yi a lamarin jam'iyya

Ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su yi amfani da damar babban zaben 2023 wajen gyara kuskuren baya, rahoton Punch.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ku amshe kasarku - Jonathan ga matasa

Har ila yau, tsohon shugaban kasar ya yi kira ga matasan Najeriya da su karbe kasarsu sannan su zamo masu lura a ayyukansu da kada kuri’u a zaben 2023.

Jonathan ya ce:

“A matsayin kasa, muna da kalubale, amma kada mu bari mu zama bayin matsalolinmu. Mu tashi mu magance matsalolin sannan mu kara gaba.
“Ya zama dole mu daidaita. Kada mu bi dabi'un da ake ganin ba daidai ba ne ya zama daidai a siyasance."

Ya kara da cewa:

“Cikin sa’a, muna a lokacin zabe. Don haka, Ina kalubalantar matasa da su dauki ragamar makomarsu ta hanyar zaben wadanda suka yarda da hadin kanmu da karfafa zaman lafiya da ci gaba, ba wadanda za su gina katangar kabilanci da rikicin addini a tsakanin mutanenmu ba.”

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Ku Zabi Mijina Domin Shine Zai Dawo Da Martabar Najeriya – Uwargidar Atiku Abubakar

A wani labarin kuma, Uwargidar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Titi Abubakar, ta roki mata da matasan Najeriya da su marawa mijinta baya a babban zaben kasar mai zuwa.

Misis Titi Abubakar ta bayyana cewa mijinta ya shirya tsaf domin ceto Najeriya sannan ya daidaita abubuwa zuwa yadda suke a baya, jaridar Punch ta rahoto.

Ta bayyana hakan ne a wajen taron kaddamar da kungiyar Atiku-Okowa Vanguard Nigeria a ranar Asabar, 3 ga watan Satumba, a babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng