Ku Zabi Mijina Domin Shine Zai Dawo Da Martabar Najeriya – Uwargidar Atiku Abubakar

Ku Zabi Mijina Domin Shine Zai Dawo Da Martabar Najeriya – Uwargidar Atiku Abubakar

  • Matar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Titi Abubakar ta nuna karfin guiwa cewa mijinta Atiku Abubakar zai farfado da Najeriya
  • Misis Titi Abubakar ta sha alwashin yiwa kananan yara da mata sha tara ta arziki idan har mijinta ya hau kujerar shugabanci a 2023
  • Ta roki mata da matasan Najeriya a kan su zabi mijinta domin makomar gobensu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Uwargidar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Titi Abubakar, ta roki mata da matasan Najeriya da su marawa mijinta baya a babban zaben kasar mai zuwa.

Misis Titi Abubakar ta bayyana cewa mijinta ya shirya tsaf domin ceto Najeriya sannan ya daidaita abubuwa zuwa yadda suke a baya, jaridar Punch ta rahoto.

Atiku da Titi
Ku Zabi Mijina Domin Shine Zai Dawo Da Martabar Najeriya – Uwargidar Atiku Abubakar Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ta bayyana hakan ne a wajen taron kaddamar da kungiyar Atiku-Okowa Vanguard Nigeria a ranar Asabar, 3 ga watan Satumba, a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar da Gwamna Wike Sun Amince da Bukata Ɗaya Kafin Fara Kamfen 2023

Titi ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Idan aka zabi mijina, zan yiwa yara da matan Najeriya sha tara ta arziki. Atiku ya yiwa mata da matasa alkawarin kaso 40 a majalisarsa, shi mutum ne mai magana daya kuma zai aikata hakan amma ku kadai ne za ku sa hakan ya yiwu.
“Ina rokonku, mata da matasanmu, kada ku siyar da tunaninku da gobenku maimakon haka, ku tsaya a kan daidai sai gobenku ya inganta saboda Atiku zai dawo da martabar da Najeriya ta rasa.”

Shettima Ya Bayyana Babban Dalili 1 Da Yasa Dole Arewa Ta Goyi Bayan Tinubu

A wani labarin, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa lokaci ya yi da arewa zata saka waAsiwaju Bola Tinubu.

A cewar Shettima yanzu ne lokacin da arewa zata biya bashin gudunmawar siyasa da dan takarar shugaban kasar na APC ke ta ba yankin tsawon shekaru da dama.

Kara karanta wannan

Bata Sallah kuma ta Tsani Mahaifiyata, Alkali Ka Taimaka Ka Raba mu, Magidanci ga Kotu

Da yake jawabi a yayin kaddamar da motocin kamfen din Tinubu/Shettima a ranar Asabar a Abuja, Shettima ya ce dan takarar shugaban kasar na APC ya sadaukar da komai nasa ga arewa, jaridar The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel