Shettima Ya Bayyana Babban Dalili 1 Da Yasa Dole Arewa Ta Goyi Bayan Tinubu

Shettima Ya Bayyana Babban Dalili 1 Da Yasa Dole Arewa Ta Goyi Bayan Tinubu

  • Yayin da zaben shugaban kasa na 2023 ke kara gabatowa, Kashim Shettima ya ce Bola Tinubu ne ya cancanci samun kuri’un Arewa
  • Shettima ya roki yan arewa da su marawa dan takarar shugaban kasar na APC baya domin ya shafe shekaru da dama yana marawa yankinsu baya
  • Shettima ya yi tuni ga yadda ya baiwa Atiku Abubakar da Nuhu Ribadu jam’iyyarsa don su nemi shugabancin kasa a karkashinta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa lokaci ya yi da arewa zata saka waAsiwaju Bola Tinubu.

A cewar Shettima yanzu ne lokacin da arewa zata biya bashin gudunmawar siyasa da dan takarar shugaban kasar na APC ke ta ba yankin tsawon shekaru da dama.

Kara karanta wannan

PDP: Yadda Shettima Yayi Zagon Kasa ga Kokarin Jonathan na Ceto 'Yan matan Chibok

Tinubu
2023: Lokaci Ya Yi da Arewa Zata Saka Wa Bola Tinubu, Shettima Hoto: @KashimSM
Asali: Twitter

Da yake jawabi a yayin kaddamar da motocin kamfen din Tinubu/Shettima a ranar Asabar a Abuja, Shettima ya ce dan takarar shugaban kasar na APC ya sadaukar da komai nasa ga arewa, jaridar The Nation ta rahoto.

Ya bayyana rawar ganin da Tinubu ya taka wajen taimakawa kudirin takarar shugabancin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a 2007, Mallam Nuhu Ribadu a 2011.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa Tinubu ne ya jagoranci nasarar Buhari a zaben shugaban kasa na 2015, Nigerian Tribune ta rahoto.

Shettima ya ce:

“A 2007 jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta muzanta tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sannan ta fatattake shi daga jam’iyyar, Asiwaju Tinubu ne ya bashi dandamalin Action Congress (AC) wanda a karkashinta ne ya yi takarar zaben shugaban kasa a 2007.

Kara karanta wannan

Tsohon Minista Ya Bayyana Halin da Lafiya 'Dan Takarar APC, Bola Tinubu, Take Ciki

“Hakazalika, a 2011, Asiwaju ya baiwa Nuhu Ribadu jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) don takarar shugaban kasa.
“A 2014, ba don Asiwaju Tinubu da ya tattara masa daukacin wakilan APC a kudu maso yamma ba, da shugaban kasa Muhammadu Buhari bai lashe tikitin takarar shugaban kasa na APC don takarar zaben 2015 ba.
“Don haka zaben 2023 zai ba arewacin Najeriya damar saka wa Tinubu da dukkan alkhairin da ya yi mata a lokuta mabanbanta.”

2023: Za A Yiwa Masu Neman Takarar Shugaban Kasa Da Sauran Mukamai Gwajin Gane Makaryata A Kyauta

A wani labarin, mun ji cewa gabannin babban zaben 2023, kamfanin Hogan Polygraph & Investigations Limited, ya bayyana shirinsa na yiwa dukkanin masu neman takarar mukaman gwamnati gwajin gano karya kyauta.

Daga cikin wadanda kamfanin ke shirin yiwa wannan gwaji, harda masu neman takarar kujerun shugaban kasa da na gwamna.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai, shugaban rukunin kamfanin, Paul Ibirogba, ya ce kamfanin zai aiwatar da hakan ne a matsayin wani hanya na tabbatar da ganin cewa al’ummar Najeriya sun zabi shugabanni masu gaskiya da halayen kirki a 2023, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Na Da Ɗan Takara? Tsohon Shugaban Kasar Ya Bada Amsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng