2023: Za A Yiwa Masu Neman Takarar Shugaban Kasa Da Sauran Mukamai Gwajin Gane Makaryata A Kyauta

2023: Za A Yiwa Masu Neman Takarar Shugaban Kasa Da Sauran Mukamai Gwajin Gane Makaryata A Kyauta

  • Wani kamfanin bincike da gano karya ya dauki nauyin yiwa masu neman takarar shugaban kasa da gwamna gwajin gane makaryata kyauta
  • Kamfanin ya ce zai yi haka ne domin tabbatar da ganin cewa yan Najeriya sun zabi shugabanni masu gaskiya da halayen kirki
  • Sai dai ya ce duk dan takarar da ya yarda da yin wannan gwaji zai saka hannu a takarda don a fitar da sakamakon gwajin a bainar jama’a

Abuja - Gabannin babban zaben 2023, kamfanin Hogan Polygraph & Investigations Limited, ya bayyana shirinsa na yiwa dukkanin masu neman takarar mukaman gwamnati gwajin gano karya kyauta.

Daga cikin wadanda kamfanin ke shirin yiwa wannan gwaji, harda masu neman takarar kujerun shugaban kasa da na gwamna.

Yan takarar shugaban kasa
2023: Kamfani Zai Yiwa Masu Neman Takarar Shugaban Kasa Da Sauran Mukamai Gwajin Gane Makaryata A Kyauta Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Da yake jawabi a wani taron manema labarai, shugaban rukunin kamfanin, Paul Ibirogba, ya ce kamfanin zai aiwatar da hakan ne a matsayin wani hanya na tabbatar da ganin cewa al’ummar Najeriya sun zabi shugabanni masu gaskiya da halayen kirki a 2023, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wike, Ortom Da Wasu Gwamnonin PDP Sun Sake Dunguma Sun Tafi Landan

Ibirogba, wanda ya bayyana cewa yan Najeriya na kara bukatar sanin gaskiya da mutunci yan siyasa ya kara da cewa gwajin gano makaryata zai taimakawa masu zabe wajen gano shugabannin da ke da ra’ayin kasa a zukatansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa yan takarar mukaman siyasa da suka yarda ayi masu gwajin gano makaryata kyauta za a bukaci su sanya hannu kan wata takarda da zai bayar da damar wallafa sakamakon gwajin ga al’umma, rahoton Thisday.

Ibirogba ya ce:

“Kamfanoni a fadin kasar nan na amfani da gwajin gano makaryata a matsayin wani makami na tsige masu neman aiki da ke da tarihin damfara domin kare kudaden shigarsu daga mahandama da kuma tabbatar da tarihin aikin mutum. Za a iya yin hakan don al’ummar Najeriya su zabi ingantattun yan takara.”

2023: Za A Gwabza Zabe Mai wahalan Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba A Tarihin Najeriya, Inji APC

Kara karanta wannan

2023: An Sake Zargin Peter Obi Da Wani Babban Abu Da Zai Iya Janyo Masa Matsala A Takarar Shugaban Kasa

A wani labarin, mun ji cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana cewa babban zaben 2023 zai zamo mafi wahala tun bayan samun yancin kan Najeriya a 1960, Daily Trust ta rahoto.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan a yayin taron yiwa Najeriya da takarar Tinubu/Shettima addu’a wanda kungiyar mata ta WIFE ta shirya a ranar Alhamis, 1 ga watan Satumba, a Abuja.

Adamu, wanda ya samu wakilcin mataimakiyar shugabar matan APC na kasa, Hajiya Zainab Ibrahim, ya ce zaben zai fi kowanne wahala ne saboda zai kasance “kimiyya tsantsa.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel