2023: "Ina Son Abin Da Obi Ke Yi, Zan Gayyace Shi Jiha Ta", In Ji Fitaccen Gwamnan APC

2023: "Ina Son Abin Da Obi Ke Yi, Zan Gayyace Shi Jiha Ta", In Ji Fitaccen Gwamnan APC

  • Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi ya bayyana so da kauna ga Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party
  • Umahi a wani shiri da aka yi kai tsaye a talabijin ya bayyana Mista Obi a matsayin abokinsa kuma yana son abin da ya ke yi game da shirin babban zabe
  • Duk da cewa ba jam'iyyarsu daya ba, gwamnan ya bayyana cewa zai gayyaci Mista Obi jiharsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gwamna Dave Umahi na jam'iyyar APC mai mulki a Jihar Ebonyi ya bayyana kaunarsa ga dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Mista Peter Obi, Daily Independent ta rahoto.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 2 ga watan Satumba yayin shirin talabijin a Arise TV lokacin da aka masa tambaya game da dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar hamayya gabanin zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Akwai Ƙulalliya Tsakanin Atiku Da Ayu, Shi Yasa Ya Ƙi Murabus, In Ji Adoke

Umahi da Obi
2023: "Ina Son Abin Da Obi Ke Yi, Zan Gayyace Shi Jiha Ta", In Ji Fitaccen Gwamnan APC. Hoto: Guardian.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Legit.ng ta tattaro, Gwamna Umahi ya bayyana Obi a matsayin abokinsa yana mai cewa yana shirin gayyatarsa jiharsa nan bada dadewa ba.

Ya ce:

"Ban taba ambaton sunan Peter Obi a maganganu na. Peter Obi abokina ne, Zan gayyace shi Jihar Ebonyi kuma za mu sanar da mutane, ina son abin da ya ke yi, kuma abin karfafawa gwiwa ne."

2023: Gwamna Umahi ya musanta cewa ya fadi maganganu marasa kyau game da Peter Obi

Gwamnan yayin hirar da aka yi da shi ya kuma yi amfani da damar ya musanta rahoton da ke cewa ya taba fadin cewa tsohon gwamnan na Jihar Anambra ba zai samu kuri'a ko daya ba a Jihar Ebonyi.

Umahi ya zargi babban jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party, PDP, da yi masa wannan sharin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yadda Na Magance Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Ɗaya, Jonathan Ya Yi Jawabi Mai Ratsa Jiki

Ya kuma bayyana cewa Igbo sun rasa damansu yayin zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam'iyyun PDP da APC.

Ka Ja Gargadi Magoya BayanKa, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci takwararsa na LP, Mr Peter Obi, ya ja kunnen magoya bayansa don su dena yada karya, makirci da aibanta shi da sauran yan takara.

Tinubu, cikin sanarwar da hadiminsa, Bayo Onanuga ya fitar, ya bukaci Obi ya gargadi magoya bayansa kuma ya bari zaben 2023 ya zama kan batutuwan da za su bunkasa kasa, cigaba da kwanciyar hankalin Najeriya, yana gargadin "karya da yada maganganu marasa tushe za ba su saka a ci zabe ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel