2023: Akwai Ƙulalliya Tsakanin Atiku Da Ayu, Shi Yasa Ya Ƙi Murabus, In Ji Adoke

2023: Akwai Ƙulalliya Tsakanin Atiku Da Ayu, Shi Yasa Ya Ƙi Murabus, In Ji Adoke

  • Tsohon Antoni Janar na tarayya, Mohammed Adoke ya ce Iyorchia Ayu, shugaban PDP na kasa ya fi damuwa da buƙatun kansa fiye da nasarar jam'iyyar
  • Adoke ya kara da cewa yana tunanin akwai ƙulaliya tsakanin Ayu da Atiku hakan yasa shugaban jam'iyyar ya ki murabus don ganin Atiku ya fadi zaben 2023
  • Rahotanni sun bayyana cewa ɗaya daga cikin sharudan da bangaren Wike suka bada don yin sulhu da Atiku shine Ayu ya yi murabus amma sai ya kira masu cewa ya yi murabus yara

Mohammed Adoke, tsohon antoni-janar na tarayya, AGF, ya ce Iyorchia Ayu, shugaban PDP na kasa, bai nuna yana son jam'iyyar ta yi nasara a zaben 2023 mai zuwa ba, rahoton The Cable.

Jigon na jam'iyyar PDP ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Shekarau: Yadda Kwankwaso Yayi Min Kwantan Ɓauna, Ya ci Amanata Daga Bisani

Shugaban PDP Iyorchia Ayu
2023: Ayu Bai Damu Da Nasarar PDP Ba, Bukatunsa Kawai Ke Gabansa. Hoto: @thecableng.
Asali: Facebook

A yayin da ake kiraye-kirayen ya yi murabus, Ayu ya yi wasu maganganu da suka ƙara dagula rikicin jam'iyyar.

Yayin hirarsa da BBC Hausa a ranar Laraba, Ayu ya ce wadanda ke cewa ya sauya daga mukaminsa yara ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Lokacin da muka fara tafiyar jam'iyyar PDP, ba mu wannan yaran ba. Yara ne wadanda ba su san dalilin da yasa muka kafa wannan jam'iyyar ba."

Ayu ya kuma ambaci sunan Adoke - wanda na hannun daman Nyesom Wike, gwamnan Rivers - a matsayin daya cikin wadanda ke cewa ya yi murabus.

Martanin Adoke

Da ya ke tsokaci kan batun, Adoke ya ce:

"Kalaman Ayu abin takaici ne kuma hakan na nuna cewa ya fi damuwa da buƙatun kansa fiye da ganin jam'iyyar ta ci zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

2023: Wani Babban Jigon APC da Dubbannin Magoya Baya Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

"Ina ganin akwai ƙulaliya tsakaninsa da ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar hakan yasa ya fi son ya ga ya sha kaye a maimakon taimakon sa ya ci zabe."

Ya cigaba da cewa:

"Idan ba haka ba, me ya sa ya dage yana son lalata Jam'iyyar ta hanyar raba kanta a maimakon hada kanta?
"Ya kamata Atiku ya farga kuma ya tashi tsaye ya yi magana na gaskiya a maimakon kananan maganganu da kiran mutane sunaye.
"Wike ba shine matsalar jam'iyya ba. Mutane su tashi tsaye kuma su fadi gaskiya a maimakon musayar maganganu."

Legit Hausa ta rahoto a baya yadda mutanen bangaren Wike suka bukaci Ayu ya yi murabus - cikin sharudan su na sulhu da ɗan takarar shugaban kasar jam'iyyar Atiku Abubakar.

2023: Bangaren Wike Ta Bada Sunan Wanda Ta Ke So A Nada Shugaban PDP Na Kasa

A wani rahoton, bangaren gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, a rikicin jam'iyyar PDP da ake yi suna bukaci a nada Taofeek Arapaja a matsayin shugaban jam'iyyar wucin gadi.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Taimaka Wa Atiku Ya Sha Kaye a Zaben 2023

Premium Times ta rahoto cewa a ranar Juma'a a yayin taron da tawagar ta yi da dan takarar jam'iyyar Atiku Abubakar, ta bukaci murabus din shugaban jam'iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, a matsayin sharadi na cigaba da tattaunawa da Atiku idan yana son goyon bayansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164