Zamu Taimaka Wa Jam'iyyar PDP Ta Sha Kasa a Zaben 2023, Gwamna Wike

Zamu Taimaka Wa Jam'iyyar PDP Ta Sha Kasa a Zaben 2023, Gwamna Wike

  • Gwamnan Ribas yace ya fahimci shugaban PDP na ƙasa na jan ragamar jam'iyya da nufin faɗuwa zaɓe a 2023 kuma zai taimaka masa
  • Gwamna Nyesom Wike ya maida wa Dr. Iyorchia Ayu, martani kan kiransu da kananan yara da basu san yadda aka kafa PDP ba
  • Jam'iyyar PDP mai adawa ta sake ɗaukar ɗumi yayin da ake gab da fara yaƙin neman zaɓe gabanin 2023

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi barazanar cewa zai taimaka jam'iyyar PDP ta sha ƙasa a babban zaɓen shugaban kasa na 2023 dake tafe.

Gwamna Wike, wanda ke takun saka yanzu haka da shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi wannan barazanar ne a wurin kaddamar da hanyoyi a yankin Omerelu, ƙaramar hukumar Ikwerri, ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Tsananta: Butulci da Girman Kai Ba Zasu Kaika Ko Ina Ba, Wike Ya Caccaki Shugaban PDP

Gwamna Wike da Iyorchia Ayu.
Zamu Taimaka Wa Jam'iyyar PDP Ta Sha Kasa a Zaben 2023, Gwamna Wike Hoto: Nyesom Wike, Iyorchia Ayu
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamnan ya yi furucin ne yayin da yake martani kan kalaman Ayu, wanda yace duk masu kira ya yi murabus ƙananan yara ne.

Da yake hira da BBC Hausa, Ayu ya yi ikirarin cewa lokacin da aka kafa PDP, waɗan nan ƙananan yaran ba su da wayo, ba su san dalilin kafa jam'iyyar ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake martani, gwamna Wike ya ayyana Dr. Ayu a matsayin mai butulci wanda ba abinda ya sa gaba sai abinda zai amfane shi kaɗai.

Ya ƙara da cewa a zahirance abinda Ayu ya sanya a gaba shi ne yadda jam'iyyar PDP zata sha kaye a zaɓen 2023 kuma a shirye yake ya taimaka masa har ya cimma burinsa.

Yara ne suka maida kai shugaban PDP - Wike

A kaƙamansa, Wike yace:

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Fallasa Babban Abinda Tinubu Ke Tsoro Game Da Atiku, Kwankwaso a 2023

"Zaka yi hasahen abinda giyar mulki zata yi da abinda butulci zai haifar, taya mutane ke zama masu butulcu a rayuwarsu. A tunani na a matsayin Ciyaman na jam'iyya wanda ke son lashe zaɓe, aikinka shi ne ka kawo zaman lafiya a jam'iyya."
"Na ɗauka aikinka shi ne ka haɗa kan jam'iyya, kar ka nuna girman kai ga jam'iyyarka. Eh (Mun ji mu yara ne), ƙananan yaran nan ne suka kai ka matsayin shugaban jam'iyya."
"Dakta Ayu yace mu kananan yara ne, To mun ji amma yaran nan ne suka tsamo ka daga kwata suka maida kai Ciyaman. Yanzu mun hangi cewa baka son jam'iyya ta lashe zaɓe, zamu taimaka maka."

A wani labarin kuma gwamna Wike ya bayyana yadda shugaban kasa da wani ministansa suka yi yunkuri tsoma baki a zaɓen Ribas

Gwamna Wike na jihar Ribas ya nuna gamsuwarsa da matakin shugaban ƙasa na tsame kansa daga zaɓen 2023 dake tafe.

Kara karanta wannan

2023: Wani Ɗan Takarar Shugaban Kasa Zai Haɗa Karfi da Atiku, Gaskiya Ta Fito

Gwamnan ya ce alƙawarin Buhari da kokarinsa na gudanar da sahihim zaɓe abun a yaba ne, amma a 2019 sun yi yunkurin shiga zaɓen Ribas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel