'Yan a Mutun Tinubu Sun Dura Wani Asibiti a Abuja, Sun Tallafawa Marasa Lafiya
- Wasu 'yan amutun Bola Tinubu sun dura asibitin Abuja, sun biya kudaden magani ga majinyata 40 da ke kwance a asibitin
- Masoyan na Tinubu sun ce sun dauki wannan kuduri ne domin tallafawa majinyatan da ke fama da fatarar biyan kudin magani a asibiti
- Sun ba majinyatan kudin a hannu ne saboda tsoron kada a murde musu hakkinkus idan kudin ya shiga hannun wasu, a cewarsu
Kubwa, Abuja - Wasu 'yan a mutun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, a ranar Alhamis, 1 ga watan Satumba, sun yi abin kirki ta hanyar biyawa majinyata 4o kudin magani a a babban asibitin Kubwa dake babban birnin tarayya, Abuja.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa masoyan na Tinubu sun yi wannan aikin ne a gaban Daraktan Likitoci, Dokta Lasisi Muyideen da wasu manyan ma’aikatan asibitin.
Da yake zantawa da manema labarai, Shola Olofin wanda ya shirya shirin tallafin kuma shugaban tawagar gangami ta Bola Ahmed Tinubu Vanguard ya bayyana kadan daga manufar wanna ba da tallafi.
Jam'iyyun siyasa da masoya 'yan takarar shugaban kasa na ci gaba da yawon neman kuri'a da kuma tallafawa masu kada kuri'u.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Garabasa: Matashi ya bude shagon aski, yana aski kyauta saboda kaunar Peter Obi
Wani matashi mai sana'ar aski a jihar Gombe ya fara yiwa mazauna yankinsu hidimar aski kyauta domin nuna goyan baya ga yakin neman zaben shugabancin kasa na Peter Obi.
Hotunan matashin da ke aski kyauta ga matasan da suka yi layi a gaban shagonsa ya bazu a shafukan sada zumunta.
A rubutun ya bayyana cewa, shagon zai yiwa jama'a aski kyauta saboda ba da gudunmawa ga nasarar Peter Obi.
Ina Hawa Mulki Zan Siyar da Kamfanin Man Fetur Din Najeriya Gaba Daya, Inji Atiku
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce ya gano irin rashawar da ake tafkawa a kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL.
Jaridar This Day ta ruwaito cewa, Atiku ya sha alwashin mai da kamfanin dungurungum sinsa hannun 'yan kasuwa domin dakile wasu abubuwan da ke faruwa a karkashinsa.
Ya bayyana wannan magana mai daukar hankali a jiya Litinin 29 ga watan Agusta yayin da ya fito a wani shirin talabijin na News Central Africa.
Asali: Legit.ng