Komawa PDP: Abin da Zan Fadawa Shekarau da Ina Kusa da Shi inji Shugaban NNPP
Shugaban Jam’iyyar PDP na Najeriya ya yi magana a game da sauya-shekar Sanata Ibrahim Shekarau da mutanensa zuwa PDP
Farfesa Rufai Ahmed Alkali yace duk abin da aka yi wa Sardaunan Kano, bai dace ya sauya-sheka daga jam’iyyarsu ta NNPP ba
A cewarsa, jam’iyyar NNPP ta karbi Shekarau da mutanensa, akasin abin da tsohon Gwamnan ya fada a matsayin dalilin shiga PDP
Abuja - Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Rufai Ahmed Alkali ya yi magana a game da sauya-shekar Ibrahim Shekarau zuwa PDP a farkon makon nan.
Rufai Ahmed Alkali ya bayyana a shirin siyasa da ake yi a gidan talabijin Trust TV a ranar Laraba, 31 ga watan Agusta, 2022 ya amsa tambayoyi a kan batun.
Farfesa Rufai Ahmed Alkali yace da yana cikin na-kusa da tsohon gwamnan na jihar Kano, da zai ba shi shawarar ya guji sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Tsohon mai ba shugaban kasar Najeriyan shawaran yace ina ma Sanata Shekarau ya yi hakuri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Gaskiyar magana, Shekarau ya rabu da wannan kujera, da ina kusa da shi, kusa da shi sosai, da na ba shi shawarar ka da yayi hakan.
Abin da yake da muhimmanci a kasar nan a wani lokacin shi ne sadaukar da kai da mutum zai yi domin cigaban daukacin Najeriya."
- Farfesa Rufai Ahmed Alkali
Ana ganin girman Shekarau a NNPP
Daily Trust ta rahoto Farfesa Alkali yana cewa yana ganin girman Shekarau, sannan Sanatan yana da alaka mai kyau da jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso.
Shugaban jam’iyyar hamayyar yake cewa NNPP ta karbi mutanen Ibrahim Shekarau da kyau, yace ko da an yi masa ba daidai ba, bai dace ya tsallaka PDP ba.
“Ko da an bata masa rai, wanda asali ma an karbe su a jam’iyya; an ba shi girman da ya kamata, kuma ina ganin kimarsa.
Kuma Shekarau yana da kyakkyawar alaka da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso; sai nayi tunanin ko me zai faru, za iyi hakuri.
Kamata yayi ya hakura, ya maida hankali a kan abubuwan da suka addabi kasarmu a yau.”
- Farfesa Rufai Ahmed Alkali
...Yadda aka yi - Kwankwaso
Kun ji labari Rabiu Kwankwaso ya yi bayanin abin da ya jawo NNPP ta rasa Malam Shekarau, duk an ba shi takarar ‘Dan Majalisar Dattawa a zaben 2023.
‘Dan takarar shugaban kasar yace rashin isasshen lokaci ya sa Shekarau ya yi korafin ba ayi adalci wajen kaso tsakanin mutanensa da 'Yan Kwankwasiyya.
Asali: Legit.ng