Katsina: APC Ta Kori Hadimin Gwamna Masari, Ta Bayyana Dalili

Katsina: APC Ta Kori Hadimin Gwamna Masari, Ta Bayyana Dalili

  • Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta sallami hadimin Gwamna Aminu Masari, Mista Aminu Lawal daga jam'iyya
  • Babagandia Abdullahi, sakataren APC na gundumar Jibia 'A' ya sanarwa manema labarai a Katsina cewa an kori Lawal ne kan cin amanar jam'iyya da zagon kasa
  • A bangarensa, tsohon mashawarcin gwamnan a bangaren koyar da sana'o'i ya rubuta wasikar murabus daga mukaminsa a gwamnatin Gwamna Masari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Jam'iyyar APC ta gundumar Jibia Ward 'A' a Jihar Katsina ta kori, mashawarci na musamman ga Gwamna Aminu Bello Masari kan koyar da sana'o'i, Mista Aminu Lawal, kan cin amanar jam'iyya.

Sakataren APC a gundumar Ward 'A', Mista Babangida Abdullahi, wanda ya sanar da korar Lawal daga APC ga manema labarai a Katsina, ya ce korar ta fara aiki nan take, This Day ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Albarka Ce' Tsohon Na Hannun Daman Buhari Ya Magantu Kan Sauya Shekar Shekarau Zuwa PDP

Tambarin APC
Katsina: APC Ta Kori Hadimin Masari Kan Zargin 'Cin Amanar Jam'iyya Da Zagon Kasa'. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Abdullahi ya yi bayanin cewa 25 cikin 27 na shugabannin gundumar sun yarda a kori tsohon karamar hukumar ta Jibia kan aikata abubuwa na cin amanar jam'iyya da zagon kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"APC a gundumar Jibia 'A' ta kori Aminu Lawal wanda ke rike da mukamin mashawarcin gwamna kan koyon sana'a saboda cin amanar jam'iyya da zagon kasa. Korarsa ta fara aiki nan take."

Martanin Lawal

Amma, Lawal bayan gano abin da jam'iyya za ta aikata ya yi murabus daga mukaminsa da gwamnatin a cikin wasikar da ya aika wa SSG na jihar, Mista Muntari Lawal.

Wasikar ajiye aikin da SSG ya same ta a ranar 29 ga watan Agustan 2022, ta ce ya yi murabus daga gwamnatin Masari daga ranar 26 ga watan Agustan 2022.

Duk da cewa tsohon mashawarcin gwamnan bai bayyana dalilin murabus dinsa ba cikin wasikar, ba za ta rasa nasaba da korarsa daga jam'iyyar APC ba da kuma rikicin da ake da tsohuwar jam'iyyarsa da PDP a jihar.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Jami'ar IBB Dake Lapai Jihar Neja Ta Janye Daga Yajin Aikin ASUU, Tace Dalibai Su Koma Aji

Binciken da This Day ta yi ya nuna cewa tsohon mashawarcin na Masari kani ne na dan takarar majalisar wakilai na tarayya na Kaita/Jibia a PDP, Mista Musa Lawal.

Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Goyi Bayan A Tsige Buhari

A wani rahoton, Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue ya goyi bayan yunkurin da majalisar dattawa na tsige Shugaba Muhammadu Buhari saboda matsalar tsaro da ke adabar kasar.

A cewar wani rahoto da jaridar ThisDay ta fitar, Gwamna Ortom na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya jinajinawa majalisar tarayyar kan wa'adin sati-shida da ta bawa shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel