2023: Komawar Shekarau PDP Albarka Ce Ga Jam'iyyar NNPP, Buba Galadima

2023: Komawar Shekarau PDP Albarka Ce Ga Jam'iyyar NNPP, Buba Galadima

  • Jigon jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, Buba Galadima, ya ce sauya shekar Shekarau Albarka ce ga jam'iyyarsu
  • Galadima, wanda a baya yana ɗaya daga cikin makusantan Buhari, ya ce Shekarau ya saba cewa an zalunce shi ya fice daga jam'iyya
  • Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya tabbatar da komawa PDP a hukumance ranar Litinin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Jigon jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, Buba Galadima, yace sauya shekar Malam Ibrahim Shekarau zuwa jam'iyyar PDP Albarka ce.

Galadima, wanda tsohon na hannun daman shugaban kasa Buhari ne, ya yi wannan furucin ne a wata hira da BBC Hausa.

A ranar Litinin da ta gabata, Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano tsawon zango biyu, ya tabbatar da komawa PDP a hukumance, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyya Ya Yarda Akwai Rikici a PDP, Ya Hango Abin da Zai Faru a 2023

Malam Ibrahim Shekarau.
2023: Komawar Shekarau PDP Albarka Ce Ga Jam'iyyar NNPP, Buba Galadima Hoto: thecableng
Asali: UGC

A makon da ya shuɗe, Shekarau, ya yi zargin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ci amanar yarjejeniyar da suka ƙulla gabanin ya amince da shiga NNPP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun hangi faruwar haka, amma tsoron da nake ji wa Shekarau Shi ne ya ɓata rawarsa da tsalle, saboda abinda mutane suka tsammaci zai aikata, bai ba su kunya ba. Duk jam'iyar da ya shiga sai yace an masa rashin adalci, sai ya fice."
"Ina mai tabbatar muku da cewa shi da ya sa ƙafa ya bar jam'iyyar mu, kashi 90 cikin 100 na magoya bayansa ba zasu bi takonsa ba, suna nan daram a NNPP. Har yau babu ɗan takarar da 'yan arewa ke ƙauna irin Kwankwaso."
"Da tserayar kuri'a ɗaya tak mutum zai iya zama shugaban kasan Najeriya, Shekarau na da kuri'u sama da ɗaya, ba son ran mu bane ya tafi amma tunda ya tafi zata iya yuwu wa hakan Albarka ce."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: An Bukaci Gwamnan Wike Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Koma Bayan Wannan Ɗan Takaran a 2023

- Buba Galadima.

Zamu maye gurbinsa a takarar Sanata - Galadima

Galadima ya ƙara da cewa kasancewar yanzun ya bar jam'iyyar su, gurbinsa ya zama ba kowa kenan don haka zasu tura wa hukumar INEC da sunan wanda zai maye gurbin, Daily Trust ta ruwaito.

"Gurbinsa ya zamo ba kowa kenan, zamu tura sako ga INEC, shi ma ya aike musu da wasika saboda haka za'a bamu dama mu maye gurbinsa."

A wani labarin kuma Abokin Takarar Tinubu Ya Sa Labule da Wani Gwamnan Arewa a Abuja

Gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya gana da tsohon gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima a gidansa dake Abuja.

Sakataren watsa labarai na gwamnan, Onogwu Muhammed, ya ce manyan jiga-jigan APC sun tattauna kan abubuwa masu muhimmanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel