Rashin Tsaro: ‘Yan Gari Sun yi Wa Shugaban Karamar Hukumarsu Ruwan Dutse

Rashin Tsaro: ‘Yan Gari Sun yi Wa Shugaban Karamar Hukumarsu Ruwan Dutse

  • Mutanen wani kauye da ake kira Dan-Gunu a garin Sarkin Pawa suna yawan fama da munanan hare-hare daga ‘yan bindiga
  • Ana zargin duk abin da ke faruwa, shugaban karamar hukumar Munye bai taba damuwa da yanayin da wannan kauye yake ba
  • A irin wannan hali ne sai Mohammed Garba Daza ya zo ta’aziyya, a nan mutanen Dan-Gunu da suke fushi da shi, suka auka masa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Niger - Labari ya zo mana cewa mutanen Dan-Gunu a garin Sarkin Pawa da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja, sun gaza hakuri kan rashin tsaro.

A rahoton da Daily Trust ta fitar a ranar Laraba, 31 ga watan Agusta 2022, an ji yadda mazauna Dan-Gunu suka yi fushi da shugaban karamar hukumar Munya.

Wadannan Bayin Allah sun koka cewa Mohammed Garba Daza bai damu da halin da suke ciki ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun farmaki kanin tsohon gwamnan wata jiha, ya tsallake

Shekara daya ba a ga Hon. Daza ba

Miyagun ‘yan bindiga sun addabi kauyen Dan-Gunu, amma ana zargin Honarabul Mohammed Garba Daza ya yi shekara daya bai kai masu ko da ziyara ba.

Ana tuhumar shugaban karamar hukumar da nuna halin ko in-kula ga talakawansa, sannan an roki shi ya taimakawa wadanda aka kai wa hari, bai iya yi ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan Neja
Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello Hoto: @AbuSBello
Asali: Facebook

Wata majiya tace mutanen Dan-Gunu suna jin haushinsa saboda duk abin da ke faruwa, bai taba kawo ziyara, ko ya taimakawa al’umma da kayan tallafi ba.

Ziyarar ta'aziyya ta kare a ature

Ana haka ne sai mutane suka samu labarin shugaban karamar hukumar ya ziyarci Dan-Gunu domin yin ta’aziyya ga wasu mutanensa da aka hallaka masu ‘yanuwa.

Da jin wannan sai wasu matasa suka dura gidan ta’aziyyar da Mohammed Garba Daza ya je domin yin gaisuwa, suka umarce shi da ya tattara ya bar masu kauye.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Wani ya yi aikin dana sani, ya kashe masoyiyarsa saboda katin ATM

Rahoton yace a nan ne mutanen wannan karkara suka nunawa shugabansu fushinsu, suka rika jifansa. Wannan abin ya faru ne a karshen makon da ya wuce.

A dalilin haka aka fasa motoci hudu a cikin tawagar Hon. Daza, shi kuma jami’an tsaro suka kubutar da shi. Jaridar tace har yanzu ba ta iya jin ta bakinsa ba.

Legit.ng Hausa ta fahimci Sarkin Pawa da wasu garuruwan da ke yankin Munya suna cikin wuraren da ‘yan bindiga suke cin karensu babu babbaka a Neja.

Matsalar wutar lantarki

Ku na da labari Kamfanin Abuja Electricity Distribution Company sun gaji da rashin cika alkawarin gwamnatin jihar Neja, sun yanke wutan gidan gwamnati.

A makon jiya aka ji kamfanin ya yankewa gidan gwamna da ma’aikatun gwamnatin Neja wuta a dalilin kin biyan wani bashin da ya haura Naira Biliyan daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng