Jerin Kananan Hukumomi 40 a Najeriya da Ba Lallai a Yi Zabe Ba a 2023
- Kananan hukumomi 40 ne akalla ake yawan kai farmaki a wasu jihohin Najeriya, kuma akwai alamun ba lallai su kada kur'u a zabe mai zuwa ba saboda ta'azzarar lamarin tsaro
- Jihohin da hakan ya shafa irinsu Kaduna da Zamfara da Imo da Neja da kuma Sokoto ne, kasancewar 'yan ta'adda sun tasa yankunan a gaba
- Duk da haka, gwamnatin Buhari na kara lasa ma jama'a zuma a baki cewa tabbas za a yi zabe a kowane yankin kasar nan
Najeriya - Ta'azzarar rashin tsaro a Najeriya ya sa 'yan kasar da dama cikin tashin hankali, kuma kullum tsoro karuwa yake a zukatan wasu da dama.
Jaridar Punch, ta ruwaito cewa, akwai kananan hukumo sama da 40 da ba lallai su kada kuri'u ba a zabe mai zuwa saboda yawaitar harin 'yan ta'adda.
Kananan hukumomin 40 suna karkashin fadin jihohin Kaduna, Zamfara, Niger, Katsina, Abia da Imo ne, kuma ga su kamar haka:
'Yan bindiga sun mamaye kananan hukumomi 8 a Kaduna
- Chikun
- Kajuru
- Kachia
- Zangon Kataf
- Kauru
- Lare
- Birnin Gwari
- Giwa
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
'Yan ta'adda da 'yan bindiga sun karbe kananan hukumomi 9 a Zamfara
- Maru
- Tsafe
- Bakura
- Anka
- Maradun
- Gusau
- Bukkuyum
- Shinkafi
- Bungudu
Boko Haram da sauran 'yan ta'adda sun kama kananan hukumomi 7 a Neja
- Rafi
- Munyan
- Shiroro
- Magama
- Mashegu
- Mariaga
- Wushishi
Kananan hukumomi 11 cikin 23 na Sokoto na fama hare-hare
- Illela
- Rabbah
- Sabon-Birni
- Isa
- Wurno
- Gada
- Goronyo
- Tangaza
- Gudu
- Denge-Shuni
- Kebbe
Kanan hukumo 5 da 'yan bindiga suka addaba a jihar Imo
- Orsu
- Orlu
- Oru East
- Oru West
- Njaba
Ba Lallai a Yi Zabe a Wasu Jihohin Arewa Maso Yamma Ba, Inji Gwamnonin Najeriya Ga Buhari
A wani labarin, wani sabon batu ya fito daga bakin gwamnonin Najeriya, inda suka bayyana ra'ayin cewa ba lallai a yi zabuka a wasu jihohin Arewa maso Yammacin kasar nan ba saboda kara dagulewar lamarin tsaro a shiyyar.
Arewa maso Yammancin Najeriya dai ta ta kunshi jihohi bakwai da suka hada da; Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, da Zamfara.
Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, gwamnonin sun bayyanawa Buhari hakan ne a wani taron kan samar da wasu ka'idoji.
Asali: Legit.ng