2023: Dan Siyasan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Bayyana Dan Takarar Da Zai Gaji Kuri'un Buhari A Arewa
- Kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na Rabiu Musa Kwankwaso, Abdulmumin Jibrin, ya yi wata hasashe kan maigidansa
- Jibrin a ranar Juma'a 26 ga watan Agusta, ya yi barazanar cewa dan takarar shugaban kasar na NNPP zai gaji kuri'u miliyan 12 na Shugaba Buhari a 2023
- Tsohon dan majalisa ya yi ikirarin cewa Kwankwaso ya kama zuciyar yan arewa kuma ba zai taba hada kai na APC ba
Abdulmumin Jibrin, kakakin yakin neman zaben Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi martani kan ikirarin da aka yi na cewa mai gidansa ya ce yan NNPP su zabi PDP.
Jibrin, cikin hirar da ya yi da manema labarai a ranar Juma'a 26 ga watan Agusta, ya ce ikirarin karya ne da wasu yan siyasa suka kirkira don neman suna, The Cable ta rahoto.
Tsohon dan majalisar na wakilai na tarayya ya ce Kwankwaso ba zai taba cewa magoya bayansa su zabi APC ko yin aiki da Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya cika baki cewa tsohon gwamnan na jihar Kano ne wanda yan arewa ke so kuma shine zai gaji kuri'u guda miliyan 12 na Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2023.
Kalamansa:
"Kwankwaso dan siyasa ne mai aiki da zahiri, ba wasa muka zo yi ba. Mun shiga takarar nan ne da gaske.
"Mutane su yi watsi da jita-jitar cewa 'Kwankwaso na yi wa Asiwaju aiki ne, cewa za mu hade da APC.
"Ta yaya zai yi hakan? Mutumin da shine ke da iko da zuciyar arewa. Mutumin da zai gaji kuri'u miliyan 12 na Buhari.
"Kwankwaso shine mutumin da ya fi fice, aka fi kauna. Shine wanda zai gaji wannan kuri'un. Yanzu ka duba yadda zaben zai kasance, babu wani gwamna mai ci yanzu a arewa da ke takarar shugaban kasa don haka ko wane gwamna yana da matsalolinsa a jiharsa.
2023: Shin Da Gaske Ne Likitan Tinubu Ya Bashi Shawara Ya Ajiye Takara? Na Hannun Daman Jagaban Ya Magantu
"Abin da ke gaban gwamnoni shine su kawo jihohinsu. Sun san cewa za su fuskanci matsala a jihohinsu idan suka juya wa Kwankwaso baya saboda mutane na tare da shi."
Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Rufe Ofishin NNPP Da Yan Sanda Suka Yi A Borno Gabanin Ziyararsa
A wani rahoton, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shuganan kasa na jam'iyyar New Nigeria People Party, NNPP, da jami'an tsaro suka yi a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, tsohon gwamnan na Jihar Kano ya yi Allah-wadai da matakin.
Asali: Legit.ng