Ai Tuni Kwankwaso Ya Gaje Farin Jinin Buhari a Arewa, AbdulMumini Jibrin

Ai Tuni Kwankwaso Ya Gaje Farin Jinin Buhari a Arewa, AbdulMumini Jibrin

  • AbdulMumini Jibrin ya ce Rabiu Musa Kwankwaso zai kwashe kuri'un da Buhari ke samu a Arewa
  • Hanarabul Jibrin yace babu dan siyasan da ya kai Kwankwaso shahara a duk fadin Arewacin Najeriya
  • Hukumar zabe ta INEC zata gudanar da zaben shugaban kasa ranar 28 ga Febrairu, 2023

Abuja - Tsohon dan majalisar wakilai kuma Kakakin yakin neman zaben jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), AbdulMumini Jibrin ya ce Kwankwaso ya gaje farin jinin Shugaba Buhari a Arewa.

Dr Musa Rabiu Kwankwaso shine dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), a zaben 2023.

Jibrin ya bayyana hakan ne a hirar da yayi a tashar Channels, TheCable ta gano.

Jibrin ya bayyana hakan yayin mayar da martani kan maganar cewa Kwankwaso na shawarar janyewa Tinubu na APC.

Ya ce babu dan takara da ya kai Kwankwaso kuri'u a Arewacin Najeriya.

Jibrin
Ai Tuni Kwankwaso Ya Gaje Farin Jinin Buhari a Arewa, AbdulMumini Jibrin Hoto: AbdMj

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Mun karyata wadannan karerayin. Kwankwaso dan siyasa ne na gaske, ba dan wani muka shiga wannan takara ba."
"Mutane suyi watsi da jita-jitan cewa Kwankwaso na yiwa Tinubu aiki. Ko zamu koma APC."
"Ta yaya zamuyi haka? Mutumin da ke da mulkin Arewa. Wanda ya gaji kuri'un Buhari milyan 12."
"Kwankwaso ya fi kowa shawara, an fi son sa. A Arewa gaba daya, babu wanda zai samu kuri'u irin na Kwankwaso."

Zamu Yi Gaskiya Wajen Tattara Kuri'u A Zabe 2023, Hukumar INEC

A wani labarin kuwa, Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta watau INEC a ranar Juma'a ta baiwa yan Najeriya tabbacin cewa za'a haska gaskiya wajen tattara kuri'u a zaben 2023.

Hukumar ta bada tabbacin cewa zata cigaba da daura sakamakon zaben kuri'u daga runfuna zuwa shafin yanar gizon jam'iyyar kamar yadda aka yi a zaben gwamnan Osun da Ekiti.

Ta baiwa yan Najeriya tabaccin cewa ba za'a yi komai a boye ba kuma kowa zai san abinda ke gudana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel