"Godiya Ta Tabbata Ga Tinubu": Tsohon IGP Ya Bayyana Yadda Tinubu Ya Masa Wata Babban Alfarma

"Godiya Ta Tabbata Ga Tinubu": Tsohon IGP Ya Bayyana Yadda Tinubu Ya Masa Wata Babban Alfarma

  • Tsohon sufeta janar na yan sandan Najeriya, IGP Mike Okiro, yana goyon bayan Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC
  • Okiro ya ce, tsohon gwamnan na Jihar Legas, shine ya taimaka wurin ganin an nada shi kwamishinan yan sandan jihar
  • Tsohon IGP din ya kuma ce Tinubu ne sanadin yi masa karin girma sau biyu daga mataimakin sifeta zuwa DIG

Lagos - Mike Okiro, tsohon sufeta janar na yan sandan Najeriya, ya ce an nada shi kwamishinan yan sanda ne saboda alfarma da Asiwaju Bola Tinubu, lokacin yana gwamnan Legas ya nema.

Okiro ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 26 ga watan Agusta wurin taron nada shi matasayin shugaban kwamitin amintattu na 'Defect Together Movement for Tinubu/Shettima 2023, Premium Times ta rahoto.

Asiwaju Bola Tinubu
"Dukkan Godiya Ta Tabbata Ga Tinubu": Tsohon IGP Ya Bayyana Yadda Tinubu Ya Taimake Shi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

2023: Shin Da Gaske Ne Likitan Tinubu Ya Bashi Shawara Ya Ajiye Takara? Na Hannun Daman Jagaban Ya Magantu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu, wanda ya yi gwamna a Legas daga 1999 zuwa 2007 shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023.

A bangarensa, Okiro ya yi aiki matsayin kwamishinan yan sanda daga 1999 zuwa 2003 kuma aka nada shi IGP a 2007.

Yadda aka tura ni aiki Legas - Okiro

Okiro ya ce IGP na wancan lokacin, Musiliu Smith ya tura shi Legas a matsayin kwamishinan yan sanda ne bayan Tinubu ya bukaci hakan.

Ya ce ya san dan takarar na APC tun lokacin National Democratic Coalition (NADECO), lokacin yana jihar Legas a matsayin mataimakin kwamishinan yan sanda, bangaren ayyuka.

A cewar Okiro, Tinubu ya nemi a dawo da shi ne a 1999 saboda kungiya Odua Peoples Congress, OPC da wasu bata gari a jihar.

Ya bayyana yadda a lokacin Tinubu ya fada wa IGP cewa "Idan kana son a samu zaman lafiya a Legas, ka turo Okiro ya dawo Legas."

Kara karanta wannan

Daga karshe: Dalilin ganawar Wike da Atiku, Tinubu, Peter Obi da Obasanjo a Landan ya fito

Akwai hannun Tinubu a karin girma sau biyu da aka min - Okiro

Okiro ya kuma ce Tinubu ne sanadin yi masa karin girma sau biyu, daga matsayin kwamishinan yan sanda zuwa mataimakin sufeta janar na yan sanda, DIG, yana cewa "dukkan godiya ga Asiwaju. Bana da haufi a zuciya ta zai maimaita abin da ya aikata a Legas."

Kalamansa:

"Tabbas Asiwaju aboki na ne. Na san shi tun lokacin ina ma'aikaci, mataimakin kwamishina (ayyuka) a Ikeja lokacin NADECO. Shi ne mai nada sarakun a NADECO. Ya fita kasar waje, ya dawo kuma ya zama gwamnan Jihar Legas.
"Ya mika bukata zuwa ga IGP (Mista Smith) - akwai matsala a Legas, laifuka sunyi yawa - fashi, kashe-kashe, garkuwa kuma OPC suna tashe. Mutane suna barin Legas. Asiwaju ya mika bukata ta musamman zuwa ga IGP. Dalilin haka na tsinci kai na matsayin kwamishinan yan sanda a Legas."

Da ya ke magana a madadin kungiyar, Umar Yakasai ya ce an zabi Okiro ne matsayin ciyaman na BoT saboda kusancinsa da dan takarar shugaban kasar na APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164