Bayan Ganawa Da Atiku A Birtaniya, Wike, Ortom Da Ikpeazu Sun Dira A Port Harcourt

Bayan Ganawa Da Atiku A Birtaniya, Wike, Ortom Da Ikpeazu Sun Dira A Port Harcourt

  • Bisa dukkan alamu, Nyesom Wike, gwamnan Jihar Rivers shine mutumin da tauraronsa ke haskawa a siyasar Najeriya
  • Bayan ganawarsu da Atiku Abubakar, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP, Wike, Samuel Ortom da Ikpeazu na Abia sun dawo gida
  • A bangare guda, wasu na kusa da gwamnan jihar Rivers sun bayyana cewa bangaren na Wike sun dage sai an cire Iyorchia Ayu kafin gwamnan na Rivers ya marawa Atiku baya

Wani rahoto da Channels TV ta wallafa ya ce Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers ya iso Port Harcourt daga kasar Birtaniya.

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue da Okezie Ikpeazu na Jihar Abia sun dawo tare da Wike a ranar Juma'a 26 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Dalilin ganawar Wike da Atiku, Tinubu, Peter Obi da Obasanjo a Landan ya fito

Wike da Atiku
Bayan Ganawa Da Atiku A Birtaniya, Wike, Ortom Da Ikpeazu Sun Dira A Port Harcourt. Hoto: @OfficialPDPng.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wike da wasu gwamnonin PDP sun gana da Atiku a daren jiya

A yayin da suke Birtaniya, gwamnonin na PDP sun gana da dan takarar shugaban kasar jam'iyyarsu, Atiku Abubakar.

Sun kuma gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

2023: PDP ko LP ko APC: Ba a san inda Wike zai fada ba

Gwamnan na Jihar Rivers, Nyesom Wike, tamkar amarya ne a baya-bayan nan a siyasar Najeriya yayin da kusan dukkan jam'iyyu ke zawarcinsa.

Wike da jihar Rivers na da muhimmanci a zaben shekarar 2023 da ke tafe. Baya ga yawan al'umma, jihar Rivers na da kudi da za ta taimaka da shi wurin kamfen.

Kuma kasancewarsa gwamna, Wike yana da duk abin da ake bukata domin shawo kan mutanen jiharsa su zabi wanda ya ke goyon baya.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar Ya Sa Labule da Gwamna Wike da Wasu Gwamnoni Uku a Landan

Idan za a iya tunawa, yayin kaddamar da gadan sama na Orochiri-Worukwo a Port Harcourt, Wike ya yi alfaharin cewa duk wanda ya yi wasa da Rivers, toh ya koka da kansa, yana mai cewa jihar za ta zabi wanda ya damu da ita ne.

2023: Girman Kanka Zai Sa Atiku Ya Fadi Zabe, Kungiya Ta Gargadi Sule Lamido

A wani rahoton, wata kungiyar siyasa mai suna 'One Nigeria Movement (ONM) ta ce girman kai da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ke yi da wasu na kusa da dan takarar PDP, Atiku Abubakar, zai sa ya sha kaye a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Kungiyar ta ce kalaman da Lamido ke furtawa a baya-bayan nan na iya raba kan kasa kuma alama ce da ke nuna cewa dan takarar shugaban kasar na PDP yana zagaye da wasu mutane da ke ganin sune kadai ke da kima.

Kara karanta wannan

Atiku ya kade: Obasanjo ya gana da Peter Obi, Wike da wasu jiga-jigai a Landan

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164