2023: Girman Kanka Zai Sa Atiku Ya Fadi Zabe, Kungiya Ta Gargadi Sule Lamido

2023: Girman Kanka Zai Sa Atiku Ya Fadi Zabe, Kungiya Ta Gargadi Sule Lamido

  • Kungiyar siyasa ta 'One Nigeria Movement' (ONM) ta ce girman kan Alhaji Sule Lamido zai sa Atiku Abubakar ya fadi zaben 2023
  • ONM ta ce kalaman da tsohon gwamnan na Jihar Jigawa ke furtawa na nuna Atiku ya zagaye kansa da mutanen da basu ganin kiman saura
  • Kungiyar ta yi martani ne kan maganganun da Lamido ya yi kan rikicin Wike da Atiku inda ya ce a kyalle gwamnan na Rivers don ba shi ke da jihar ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Port Harcourt - Wata kungiyar siyasa mai suna 'One Nigeria Movement (ONM)' ta ce girman kai da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ke yi da wasu na kusa da dan takarar PDP, Atiku Abubakar, zai sa ya sha kaye a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Kungiyar ta ce kalaman da Lamido ke furtawa a baya-bayan nan na iya raba kan kasa kuma alama ce da ke nuna cewa dan takarar shugaban kasar na PDP yana zagaye da wasu mutane da ke ganin sune kadai ke da kima.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Ganawar Wike Da Tinubu, Atiku Ya Nufi Landan Don Shawo Kan Gwamnan Na Rivers

Sule Lamido
2023: Girman Kanka Zai Sa Atiku Ya Fadi Zabe, Kungiya Ta Gargadi Sule Lamido. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar da shugaban kungiyar, Ahmed Sodiq-Mugoro da sakatarenta Babatunde Aliyu suka fitar a ranar Laraba, na cewa abubuwan da Lamido, wanda ya haura shekaru 70 ke fada a Channels Television alama ce da ke nuna na kusa da Atiku ba su son ya ci zabe.

Munafinci ne Lamido ya bude baki ya kira Wike sarki, Kungiyar ONM

Kungiyar ta kuma ce kirar Wike da sunan Sarki da Lamido wanda bayan ya yi gwamna na shekara takwas ya kakaba wa PDP dansa a matsayin dan takara munafunci ne, The Eagle Online ta rahoto.

Ta ce abin kunya ne matashin gwamna kamar Wike ya iya kame bakinsa yayin da dattijo wanda ya haura shekaru 70 kamar Lamido ya rika magana babu lissafi.

Lamido yace mambobin tawagar Atiku da Wike da suka gana a Port Harcourt, Jihar Rivers kawai masu yi wa jam'iyya fatan alheri ne kuma ba a sansu a jam'iyya ba.

Kara karanta wannan

Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015

A martanin, ONM ta ce bisa alamu Atiku da wadanda ke kusa da shi kamar Lamido ba su son Wike da mutanensa. Wadanda ke tare da Atiku mutane ne da ke ganin kamar suna da kuri'u a aljihunsu kawai jira suke yi a sanar da shi (Atiku) matsayin shugaban kasa.

Amma, munyi imanin cewa ko ka san ka ci zabe, ba sai ka shafa wa abokan hammayarka a fuska ba kafin zabe da bayyana sakamako, ta hanyar yawo a kafafen wasta labarai kana magana kamar wasu ba su da muhimmanci.

ONM din ta ce daga irin maganganun da mutanen da ke kusa da Atiku ke fada, Wike na iya gani karara cewa ba za a mutunta yarjejeniya da za su yi ba, don haka su dena kokarin sulhu da Atiku da mutanensa.

Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015

A wani rahoton, gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya yi shagube ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, yana mai cewa ba shi da wata tasiri a siyasar yanzu, The Punch ta rahoto.

Lamido yayin da ya ke magana a shirin Politics Today na Channels Television a daren ranar Talata ya ce babu bukatar yin sulhu tsakanin Wike da Atiku Abubakar domin babu wanda ya yi wa gwamnan na Rivers laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel