Za a Shiga Zaben 2023, Sunan ‘Dan takaran APC Ya Canza, Ahmad Ya Koma Aminu

Za a Shiga Zaben 2023, Sunan ‘Dan takaran APC Ya Canza, Ahmad Ya Koma Aminu

  • Sunan ‘Dan takaran APC a mazabar Babura da Garki a Jihar Jigawa ya rikide, don haka aka je kotu domin hana shi zabe
  • Lauya ya fadawa Kotun tarayya cewa ‘Dan siyasar ya canza suna, ya tashi daga Aminu Kanta zuwa Ahmed Muhammad
  • Kafin zaben fitar da gwani, ‘dan takaran yana amfani da Ahmed Mohammed, yanzu sunansa ya dawo Aminu Kanta

Abuja - An roki Alkalin kotun tarayya da ke zama a garin Abuja, Emeka Nwite ya hana Aminu Kanta tsayawa a matsayin ‘dan takara a zaben 2023.

Jaridar Leadership ta fitar da rahoto a safiyar Alhamis, 25 ga watan Agusta 2022, inda akaji labari Isa Dogonyaro ya shigar da kara a gaban kotun Abuja.

Isa Dogonyaro ta hannun Lauyansa watau Sunusi Musa ya roki kotu ta hana Aminu Kanta shiga zaben 2023 a matsayin ‘dan takaran jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Mu ba butulu bane: Tinubu ne zan gaji Buhari a 2023, Insha Allahu, Masari ya bayyana dalilai

Kanta yana neman kujerar ‘dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Babura da Garki a Jigawa.

A wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1052/2022, Lauyan Dogonyaro ya fadawa kotu cewa akwai matsala a tattare da sunan wanda ake tuhuma.

Ahmad aka sani a Jigawa

An rahoto Sunusi Musa yana cewa Aminu Kanta yayi amfani da sunan Ahmed Mohammed ne a lokacin da yake rike da mukami a gwamnatin Jigawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majalisar Wakilai
'Yan Majalisar Wakilan Najeriya Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

Tsakanin 2015 da 2022, Kanta ya rike kujerar Kwamishina a gwamnatin Badaru Abubakar, daga baya ya zama Mai taimakawa gwamnan jihar Jigawa.

Korafin da ake yi shi ne Aminu Kanta ya shiga zaben fitar da gwani da suna na dabam da wanda aka san shi a lokacin yana mai ba Gwamna shawara.

Lauyan da ya tsayawa Doganyaro yace a ranar 16 ga watan Mayun 2022 ne Ahmad ya yi murabus, sai a ranar 28 ga wata ya shiga zaben APC da sunan Kanta.

Kara karanta wannan

INEC Ta Kwantar da Hankalin Jama'a, Tace Murde Zaben 2023 Ba Zai Yiwu Ba

Takardun makaranta sun yi gardama

Rahoton jaridar Blueprint ya nuna cewa Lauyan da ya shigar da kara ya bukaci a duba kwan-gaba-kwan-baya da ‘dan takaran ya yi wajen cike fam din INEC.

Aminu Kanta (Ahmed Mohammed) ya fadawa hukumar zabe cewa ya kammala makarantar firamare tun 1976, amma sai a 2018 ya iya gama sakandare.

Buhari ya yi wa 'yan takara gargadi

Kun ji labari Muhammadu Buhari ya nuna ba zai mara baya ga har ‘Danuwansa da tsofaffin Hadimansa da suka fice daga jam’iyyar APC mai mulki ba.

Shugaban Najeriyan ya ja-kunnen har ‘Yan APC da suke shari’a da ‘yan takaran jam’iyya, yace wadannan ‘yan siyasa su karata can a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel