Bayan Ganawar Wike Da Tinubu, Atiku Ya Nufi Landan Don Shawo Kan Gwamnan Na Rivers
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a zaben shekarar 2023 Atiku Abubakar ya tafi Landan don ganawa da Nyesom Wike
- Hakan na zuwa ne kimanin kwana guda bayan rahotanni sun bayyana cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan na Rivers don zawarcinsa
- Tun dai bayan zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na PDP aka rika samun rashin jituwa tsakanin Atiku Abubakar da Wike wanda ya sha kaye a zaben kuma aka ki zabensa mataimakin shugaban kasa
Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP, ya garzaya Birtaniya a wani yunkuri na warware rikicinsa da Wike, gwamnan Jihar Rivers, The Cable ta rahoto.
Majiyoyi na kusa da tsohon mataimakin shugaban kasar sun ce Atiku na shirin ganawa da gwamnan na Rivers ne a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce:
"Dan takarar shugaban kasar na PDP ya kama hanyar zuwa Landan bayan ya dawo daga Paris jiya. Ana shirin zai gana da Wike gobe don yunkurin yin sulhu da shi."
Kuma, makusantan dan takarar shugaban kasar na PDP ba su ji dadin yadda Sule Lamido, tsohon gwamnan Jihar Jigawa, da Babangida Aliyu, tsohon gwamnan Jihar Niger, suka rika sukar Wike kuma suna son Atiku ya ja masa kunne, wani majiyar ya ce.
A hirar da aka yi da shi a Channels TV a ranar Talata, Lamido ya ce:
"Mu manta da Wike."
Tsohon gwamnan na Jihar Jigawa ya kara da cewa:
"Wike mutum daya ne, bana tunanin domin shine gwamna a jihar, shi ke da juya dukkan mutanen Rivers."
Yunkurin na Atiku na yin sulhu da Wike na zuwa ne kwana guda bayan Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasar APC ya gana da Wike a Paris, Faransa.
Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue; Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ikpeazu na Jihar Abia, da wasu jiga-jigan PDP masu goyon bayan gwamnan na Rivers sun hallarci taron.
Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015
A bangare guda, Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya yi shagube ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, yana mai cewa ba shi da wata tasiri a siyasar yanzu, The Punch ta rahoto.
Lamido yayin da ya ke magana a shirin Politics Today na Channels Television a daren ranar Talata ya ce babu bukatar yin sulhu tsakanin Wike da Atiku Abubakar domin babu wanda ya yi wa gwamnan na Rivers laifi.
Asali: Legit.ng