Kar a Wani Sako NNPP a Hayaniyar Shekarau da Kwankwaso, Inji Shugaban NNPP

Kar a Wani Sako NNPP a Hayaniyar Shekarau da Kwankwaso, Inji Shugaban NNPP

  • Shugaban jam'iyyar NNPP na kasa ya bayyana kadan daga manufar jam'iyyar a zaben 2023 mai zuwa
  • Alkali ya ce sam bai kamata a dauko batun sauya shekar Shekarau da jam'iyyar NNPP ba, saboda wasu dalilai
  • Shekarau ya sauya daga jam'iyyar NNPP a ranar Litinin din da ta gabata, lamarin da ya jawo cece-kuce

Jihar Legas - Shugaban jam'iyyar NNPP na kasa, farfesa Rufa’i Alkali, ya ce jam’iyyar ba zai yiwu a jefa jam'iyyar cikin cece-kuce ba saboda yunkurin ficewar Shekarau daga cikinta.

Shekarau, wanda tsohon dan APC ne ya zama jigon NNPP cikin kankanin lokaci tun bayan komarsa jam'iyyar a watan Mayun bana, Daily Nigerian ta ruwaito.

A ranar Litinin, 22 ga watan Agusta ne Mallam Shekarau ya ayyana ficewarsa daga NNPP saboda rashin ba magoya bayansa gatan da ya cancanta a jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin PDP, Na Hannun Daman Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC

Kada ku sanya NNPP a rigimarku, inji shugaban NNPP
Kar ka wani sako NNPP a hayaniyarka da Kwankwaso, inji shugaban NNPP | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Da yake martani game da ficewar Shekarau, Alkali ya shaida wa manema labarai a Legas a ranar Laraba cewa jam’iyyar ta mutunta shawarin Shekarau.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kada a jawo NNPP batun ficewar Shekarau daga jam'iyya

A cewarsa:

“Game da Shekarau, muna mutunta shawarinsa, amma ba za mu bari a yi ta ririta sunan jam’iyyar NNPP kan rigimar da bata da makama.
“Muna ba shi girma sosai kuma mutum ne da ya ke da mafarkin ci gaban kasar nan. Muna mutunta shawarinsa."

A bangare guda, ya ce har yanzu jam'iyyar na ci gaba da tuntubar Shekarau don duba yiwuwar sulhu.

Hakazalika, Alkali ya bayyana kadan daga manufar jam'iyyar NNPP, inda yace za ta tabbatar da inganta tsaro a Najeriya idan ta samu dama, The Guardian ta ruwaito.

Game da tattalin arziki, Alkali ya ce NNPP za ta inganta tattalin arzikin Najeriya cikin kankanin lokaci.

Kara karanta wannan

Sai an gyara: Shugaba a PDP Ya Yarda Akwai Zalunci a Jam’iyya a Rabon Kujeru

Dalilin da yasa na fice daga NNPP, na raba kaina da tafiyar Kwankwaso, bayanin Shekarau

A wani labarin, bayan sauka da motar jam'iyyar NNPP mai alama kayan marmari, Mallam Ibrahim Shekarau ya bayyana dalilan da suka sa yi watsi da jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Sheakau dai shi ne sanata mai wakiltar Kano tsakiya a majalisar dattawa, kuma ya fice daga APC bayan rasa tikitin komawa takara, inda ya koma NNPP aka bashi tikitin.

Shekarau ya bayyana cewa, yanke fice daga NNPP ne biyo bayan hana magoya bayansa foma-fomai tsayawa takara a zaben 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.