Hantar Atiku da PDP Ta Kada Bayan Samun Bayanin Zaman Tinubu da Wike a Landan
- ‘Dan takaran APC a zaben 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mutanensa sun yi taro da Gwamna Nyesom Wike a boye a Kasar Ingila
- An fahimci cewa an tattauna da Nyesom Wike ne a kan yadda zai taimakawa jam’iyyar APC a zaben shugaban Najeriya da za ayi a badi
- Kowane bangare ya zo da mutum uku inda Gwamnoni hudu (na Ekiti, Legas, Oyo, Benuwai) suka wakilci tsagin Bola Tinubu da na Wike
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
London - Zaman da aka yi a birnin Landan a kasar Ingila tsakanin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Nyesom Wike ya tada hankalin jam’iyyar PDP.
Rahoton Daily Trust na ranar Laraba, 24 ga watan Agusta 2022, ya bayyana cewa wannan zama da aka yi ya birkita PDP da ‘dan takaranta na zabe mai zuwa.
Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa a wannan zama da aka yi a ranar Litinin a kasar Ingila, an tattauna kan abin da ya shafi takarar Bola Tinubu a zaben 2023.
Kamar yadda rahoton ya nuna, mutane shida suka yi wannan zama. Gwamna Wike ya kawo mutum uku daga bangarensa, shi ma Tinubu ya kawo mutum uku.
Taro ya yi kyau inji wata majiya
Wani wanda yake bangaren Bola Tinubu ya tabbatar da cewa zaman ya haifar da da mai ido.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daga bangaren ‘dan takaran na APC akwai Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu sai kuma Mai girma Kayode Fayemi mai shirin barin mulkin jihar Ekiti.
A gefe guda, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai da kuma Gwamnan jihar Oyo watau Seyi Makinde ne suka wakilci tsagin Wike a wajen wannan zama.
Wani tsohon Ministan da ke tsagin Wike ya shaida cewa babu wani laifi don sun gana da Tinubu domin a cewarsa, Atiku ma ya hadu da gwamnonin APC.
Me aka tattauna a zaman?
Abin da aka tattauna a taron shi ne ko Gwamnan na Ribas zai fice daga PDP ko kuma za iyi zamansa a jam’iyyar, amma ya taimakawa APC a zabe mai zuwa.
Irinsu Sanata Adeseye Ogunlewe sun ba Wike shawarar ya bar jam’iyyar PDP domin ba a ganin darajarsa a nan, ya fada masa ya hada-kai da su a tafiyar APC.
Da aka tuntubi Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Paul Ibe kan batun, ya ki cewa komai. Haka zalika an nemi jin ta bakin APC, amma duk ba a dace ba.
Ina Wike ya sa gaba?
Kuna da labari tun da Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya sha kashi a zaben tsaida ‘dan takaran shugaban kasa a hannun Atiku Abubakar, aka rasa gane kan shi.
Wike ya hadu da Peter Obi mai neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar LP. Sai ga shi yanzu ana ji cewa ya gana da ‘dan takaran APC a birnin Landan.
Asali: Legit.ng