Za Ayi Kawance Tsakanin APC da 'Dan takaran NNPP, A Doke PDP a Akwa Ibom
- Ba abin mamaki ba ne ‘ya ‘yan jam’iyyar APC su bi bayan John Akpanudoedehe a zaben gwamnan jihar Akwa Ibom da za ayi a 2023
- Etim Etim wanda su ne manya a APC na reshen jihar Akwa Ibom, ya nuna za su karbi John Akpanudoedehe a matsayin ‘dan takaransu
- Tsohon sakataren APC na kasa shi ne yake yi wa NNPP takarar Gwamna a Akwa Ibom, ita kuma jam’iyyar APC ba ta da ‘dan takara
Akwa Ibom - Akwai yiwuwar a ga cewa a 2023, jam’iyyar APC ta karbi ‘dan takaran NNPP a zaben gwamnan jihar Akwa Ibom, John Akpanudoedehe.
A ranar Talata, 23 ga watan Agusta 2022, Premium Times ta rahoto wani jagora a jam’iyyar APC yana cewa watakila su bi Sanata John Akpanudoedehe.
Jam’iyyar APC mai mulki ta samu kan ta a matsala a jihar Akwa Ibom domin hukumar INEC ba ta san da zaman ‘dan takararta, Akanimo Udofia ba.
Hukumar zabe tace ba ta da masaniyar tsaida Udofia a matsayin ‘dan takara. Abin da hakan ke nufi shi ne APC ba ta da damar shiga zaben gwamna a jihar.
Za ayi shinkafa da wake a 2023?
Etim Etim, wani jigo a APC ta reshen Akwa Ibom ya yi magana a shafinsa na Facebook a makon da ya wuce, ya na jin ra'ayin jama'a a game da 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda Etim Etim ya fada, jagororin jam’iyyar APC sun tsaida cewa za su bada goyon bayansu ga John Akpanudoedehe na NNPP a takarar Gwamna.
Don Etiebet yana tare da Akpanudoedehe
‘Dan siyasar yake cewa da zarar lokacin kamfe ya karaso, za su yi gangami domin nuna goyon bayansu ga Akpanudoedehe wanda ya samu takara a NNPP.
Amma jaridar tace Etim bai iya fadan a ina aka yi wannan zama ba, da APC ta yarda da wannan. A cewarsa, Don Etiebet ya nuna za a bi NNPP ne a zaben badi.
“Da zarar INEC ta rufe kofar tsaida ‘yan takara, kuma an soma kamfe na gwamna (a ranar 12 ga watan Oktoba), APC za ta shirya gangami a Uyo domin karbar Akpanudoedehe a matsayin ‘dan takaranmu.”
- Etim Etim
Akpanudoedehe zai kai labari a 2023?
Etiebet wanda ya yi Ministan fetur na tarayya a gwamnatin soja, yana cikin manyan magoya bayan Akpanudoedehe wanda ya rike sakataren APC na kasa.
Tsohon sakataren na APC ya yi takarar gwamnan Akwa Ibom a ACN a 2011, ya sha kasa a wajen Godswill Akpabio. A 2022 ya koma NNPP da ya rasa tikiti.
Atiku ya fara shirin kamfe
Dazu kun ji labari Atiku Abubakar da jam’iyyar hamayya ta PDP sun kammala shirin kafa kwamitin yakin neman kujerar shugabancin kasa a zaben 2023.
Ana tunani rigimar da ta kunno kai a jam’iyyar adawar ta hana tun tuni an san wadanda za su taya Alhaji Atiku Abubakar yakin zama shugaban kasa.
Asali: Legit.ng