2023: Tsohon Gwamna Ya Fadawa Atiku Abin da Zai Yi Idan Yana Son Cin Zabe

2023: Tsohon Gwamna Ya Fadawa Atiku Abin da Zai Yi Idan Yana Son Cin Zabe

  • Jonah Jang ya yi kira da babban murya ga ‘Dan takaran Shugaban kasa a PDP da ya dinke barakarsa da mutanen Nyesom Wike
  • Sanata Jonah Jang ya ce dole sai Alhaji Atiku Abubakar ya sasanta da su, sannan zai samu damar lashe zaben shugabancin kasa
  • Jang yana cikin wadanda suka marawa Wike baya a zaben fitar da gwanin PDP, amma a karshe Atiku ya samu tikitin zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Plateau – Mun ji labari cewa tsohon gwamna a jiha Filato, Jonah Jang ya yi kira ga Alhaji Atiku Abubakar da yayi sulhu da Gwamna Nyesom Wike.

The Cable ta rahoto Sanata Jonah Jang yana cewa idan ‘dan takaran shugaban kasar ya sasanta da Gwamnan Ribas, PDP za ta ci babban zaben 2022.

Jonah Jang ya yabi Gwamna Wike wanda yace gwamnatinsa ta kawo abubuwan more rayuwa da al’umma ba su taba ganin irinsu ba a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya Jero Abubuwan da za su Hana Atiku Abubakar Samun Nasara a 2023

Sanatan na Arewacin Filato ya ziyarci Ribas ne domin kaddamar da wasu tituna da aka yi a garin Omagwa, a nan ne ya ba Atiku shawarar ya yi sulhu.

Tsohon gwamnan ya kuma dauki lokaci wajen yabawa Wike a kan neman takarar shugaban kasa da ya yi da goyon bayan da ya rika ba PDP tun 2015.

“Ina kira ga ‘dan takarar shugaban kasarmu ya dinke baraka da dukkanin wasu ‘ya ‘yan jam’iyya, musamman mutanenka (Wike)

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ni ma ina alfaharin zama a cikinsu. Yin wannan zai tabbatar da nasara a zaben 2023.”

- Jonah Jang

Wike.
Nyesom Wike tare da Dr Olusegun Mimiko Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

A cewar tsohon gwamnan na Filato, babu yadda za ayi PDP ta kai labari ba tare da bangaren Wike ba, wanda su ne suka rika ba jam’iyyar gudumuwa.

“Kamar yadda na fada, wadannan mutane sun yi kokari wajen kafa jam’iyyar nan, saboda haka ba za a iya watsi da su kurum a rana daya ba.

Kara karanta wannan

Ana Za a Bar Mulki, Tsohon ‘Dan Majalisa yace Ganduje Bai Ci Zaben 2019 ba

Mu na bukatar mu hada-kai, mu ajiye sabaninmu ta hanyar fahimtar duk mu na bukatar junanmu domin yin nasara a babban zabe na kasa.”

- Jonah Jang

APC ta kashe kasa - Jang

Jaridar This Day ta ce Jang wanda ya yi gwamna tsakanin 2007 da 2015 ya soki gwamnatin Muhammadu Buhari a kan lamarin tabarbarewar arziki.

Duk da yadda abubuwa suka tabarbare, Sanata Jang yace Wike ya kawowa mutanen Ribas cigaba.

Silar rikicin Atiku v Wike

An samu labari Osita Okechukwu yace sabawa tsarin Jam’iyyar PDP da aka sani tun 1999 na karba-karba shi ne sanadiyyar rikicin cikin gidan PDP a yau.

Ganin yadda ‘Yan Arewa suka zabi Nnmadi Azikwe, Olusegun Obasanjo da MKO Abiola, Okechukwu yana ganin Atiku Abubakar ba zai iya cin zabe ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel