Irin Mulkin da Muka Yi a Borno da Legas, Shi Za Mu Yiwa Najeriya, Inji Abokin Takarar Tinubu
- Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana irin ayyukan da za su yiwa Najeriya
- Kashim Shettima ya ce irin abin da yayi a Borno da kuma abubuwan da Tinubu ya yi Legas su za su maimaita a Najeriya
- Jam'iyyun siyasar Najeriya na ci gaba da shirin 2023, 'yan takara na fadin alkawarun da za su yiwa 'yan kasa idan aka zabe su
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Legas - Abokin takarar Tinubu a zaben 2023, Kashim Shettima ya bayyana irin tagomashin da suka shiryawa 'yan Najeriya, Channels Tv ta ruwaito.
Shettima ya ce, abubuwan mamaki da Bola Tinubu ya yi jihar Legas sadda yake gwamna su ne za su kasance a Najeriya bayan 2023.
Hakazalika, ya ce za su surka da irin ababen da ya yiwa jihar Borno, domin ganin an samu ci gaba a Najeriya.
Shettima dai tsohon gwamnan jihar Borno ne, shi kuwa Tinubu tsohon gwamnan jihar Legas, kuma a yanzu su ke rike da tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, haka nan Daily Post ta ruwaito.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake jawabi a bikin bude taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyi ta Najeriya na 2022 da aka gudanar a Otal din Eko and Suites da ke Legas, ya ce, suna da yakinin samar da sauyi nagari a Najeriya.
Ya ce:
“Saboda haka, za mu dabbaka irin nasarorin da muka samu a Legas, a Borno da kuma wasu jihohin da ke gaba-gaba ta yadda kasarmu za ta inganta."
Sauran wadanda suka halarci taron
Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP na daya daga cikin wadanda suka haralci taron.
Hakazalika, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi shi ma ya halarta tare da sauran jiga-jigan siyasar Najeriya.
Jihar Borno ce inda lamurran ta'addan Boko Haram suka fara a shekarar 2009.
Barnar Boko Haram na tsawon shekaru 13 ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama 40,000 tare da raba mutane sama 2.2m a yankin Arewa maso Gabas, kuma ita ce jihar da Shettima ya mulka.
Kowa da Irin Nasa Kokarin, Shugaba Buhari Ya Yi Iyakar Kokarinsa, Inji Isa Yuguda
A wani labarin, yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da kokawa game da mulkin Buhari, tsohon gwamnan Bauchi ya yaba da irin kokarin da Buhari ya yi shekarun mulkinsa.
Ya bayyana yabonsa ne ga Buhari a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels a shirin Sunrise Daily.
Isa Yuguda, ya ce shugaba Buhari ya yi iyakar kokarinsa idan aka yi duba da lamurran tsaro da kuma kalubalen da Najeriya ke fuskanta.
Asali: Legit.ng