Jigon APC ya Jero Abubuwan da za su Hana Atiku Abubakar Samun Nasara a 2023
- Osita Okechukwu ya yi fashin baki a game da rikicin jam’iyyar PDP da kuma takarar Atiku Abubakar a zabe mai zuwa na 2023
- Shugaban na VON ya bayyana cewa babu adalci a takarar da Atiku Abubakar ya samu, ya kuma ce bai kamata ya lashe zabe ba
- ‘Dan siyasar yace PDP ba za ta ci zabe ba domin mutanen Arewa – inda Atiku ya fito, ba za su ba shi kuri’a a zaben shekarar badi ba
Abuja – Shugaban VON, Osita Okechukwu, ya zargi Atiku Abubakar da cewa bai cika jagoran hadin-kai ba, tun da ya sabawa tsarin karba-karba.
The Cable ta kawo rahoto Darekta Janar na VON din ya yi wannan tsokaci ne yayin da ‘yan jarida suka yi masa wasu tambayoyi a Abuja.
Da yake bada amsa a ranar Lahadi, 21 ga watan Agusta 2022, Osita Okechukwu ya ce saba tsarin karba-karba ne ya haddasa rigimar cikin PDP.
A ra’ayin Okechukwu, da kamar wuya Atiku Abubakar ya yi nasara a zaben 2023 saboda wasu na ganin ya kamata shugabanci ya fito ne daga Kudu.
‘Dan siyasar yake cewa Atiku ba jagoran hadin-kai ba ne, sannan ba zai iya yin galaba aan kungiyar gwamnoni da Shugaba Muhammadu Buhari.
Sauran wadanda ba su tare ‘dan takaran na PDP sun hada Olusegun Obasanjo, Edwin Clark, da Ayo Adebanjo, baya ga talakawan Arewa masu zabe.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Atiku zai raba kan Arewa da Kudu?
Jagoran na APC yake cewa manufar Atiku Abubakar ita ce raba kan ‘Yan kudu da kuma Arewa. Okechukwu yace PDP ba za ta samu kuri’un Arewa ba.
“Kuskure ne ya yi tunanin zai yaudare mu da sunan shi ne jagoran hadin-kai daga Arewa. Mutanen Arewa na da wayewa, sun zabi Zik, Abiola da Obasanjo.”
“Ko ka yarda, ko ka da ka yarda, babban rikicin Wike da Atiku shi ne sabawa dokar PDP, dabarar da Aminu Rambuwal ya yi masa da kuma rauninmu.”
Independent ta rahoto ‘dan siyasar yana cewa duk abin da zai faru, PDP ba za ta ci zabe ba.
'Yan kishin kasa sun yi wahalar banza
Okechukwu yana ganin idan Atiku Abubakar ya samu mulki, sauran ‘yan Arewa da suka hakura da burinsu na karbar shugabanci a baya, sun yi asarar banza.
Yake cewa irinsu Abubukar Rimi, Umaru Shinkafi, Adamu Ciroma, Sola Saraki sun hakura da takarar shugabancin kasa a 1999, saboda mulki ya koma Kudu.
Ba daidai ba ne mulki ya dawo Arewa
An ji tsohon jigon PDP wanda yanzu ya na jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode ya fito gadan-gadan yana goyon bayan Bola Tinubu a babban zaben shekarar 2023.
Shekarun baya Cif Fani-Kayode yana cikin wadanda suka fi kowa ragargazar gwamnatin Muhammadu Buhari, yanzu ya dawo daga rakiyar tafiyar PDP.
Rikicin Atiku Da Wike: PDP Za Ta Rasa Mambobi Da Dama A Yayin Da Jerry Gana Yayi Barazanar Fita Daga Jam'iyyar
Asali: Legit.ng