Ba Mu Da Shirin Tsige Gwamna El-Rufai Daga Kujerarsa, Kakakin Majalisar Kaduna

Ba Mu Da Shirin Tsige Gwamna El-Rufai Daga Kujerarsa, Kakakin Majalisar Kaduna

  • Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Zailani, ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo cewa suna shirin tunɓuke gwamna El-Rufai
  • A wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Zailani ya kuma musanta cewa alakarsa da gwamna ta yi tsami
  • A ranar Lahadin nan, batun da ke cewa majalisar Kaduna na shirin tsige El-Rufa'i ta ya yi tashe a kafafen sada zumunta

Kaduna - Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Honorabul Yusuf Zailani, ya musanta duk wani shiri da ake yaɗawa cewa mambobin majalisa na yi da nufin tsige Gwamna Malam Nasiru El-Rufai.

Shugaban majalisar ya ayyana raɗe-raɗin tunɓuke gwamnan kan tugume-tuhumen da suka shafi cin hanci da rashawa da labarin ƙarya mara tushe, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Rahoton shirin mambobin majalisa na tsige gwamna ya karaɗe kafafen sada zumunta ranar Lahadi, 21 ga watan Agusta, 2022.

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai.
Ba Mu Da Shirin Tsige Gwamna El-Rufai Daga Kujerarsa, Kakakin Majalisar Kaduna Hoto: The Governor Of Kaduna/facebook
Asali: Facebook

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Ɗahiru Ɗanfulani, ya fitar, Zailani ya kuma ƙaryata rahoton da ke cewa yanzu majalisar na gudanar da bincike kan kashe-kashen kuɗin ma'aikatu da hukumomin gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwan ta ce:

"Hankalin shugaban majalisar dokokin Kaduna ya kai kan wani rahoto na shirin tsige Gwamna Malam Nasiru El-Rufai da ke yawo a kafafen sada zumunta."
"A saukake wannan aikin tsagin yan adawa ne da maƙiyan cigaba da ɗasawa tsakanin ɓangaren masu doka da majalisar zartaswa karkashin jagorancin Malam Nasiru El-Rufai."
"Suna haka ne da nufin ta da yamutsi tsakanin ɓangaren zartarwa da majalisa domin hana mutanen Kaduna cigaba da shan romom demokaraɗiyya da suke amfana da shi saboda kyakkywar alaƙar ɓangarorin biyu."

Shin dagaske alaƙa ta yi tsami tsakanin Kakaki da El-Rufai?

Haka zalika Sanarwan ta yi fatali da jita-jitar cewa alaƙa ta yi tsami tsakanin shugaban majalisar da Gwamnan Kaduna, kamar Tribune ta rahoto.

"Haka nan rahoton da ke ikirarin alaƙar gwamna da kakakin majalisa, Yusuf Zailani, ta yi tsami a yanzu ba komai bace illa shaci faɗi da gurɓataccen hangen mai rubutu da masu ɗaukar nauyi."
"Saboda haka ina mai bayyana cewa baki ɗaya jita-jitar shiryayyar ƙeta ce da nufin gurɓata tunanin mutane kuma ya kamata kowa ya yi fatali da ita."

A wani labarin kuma tsohon kakakin majalisar tarayya ya aike da sako ga IGP, ya fallasa Sunayen mutanen har da yan sanda

Yakubu Dogara ya aike da korafi ga Sufeta Yan sanda na ƙasa kan wasu da ake zargin suna kulla shirin raba shi da rayuwarsa.

Tsohon kakakin majalisar tarayyan ya bayyana sunayen yan sanda uku da suka yi kokarin siyarwa wani bindiga da nufin kashe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel