CBN ta saki Dala Miliyan 210 a kasuwar canji a makon yau

CBN ta saki Dala Miliyan 210 a kasuwar canji a makon yau

- Babban bankin Najeriya ta saki Daloli a kasuwar canji

- CBN ta dumbuzo har Dala Miliyan 210 ga masu bukata

- Wannan ne yake hana farashin Dala yayi wawan tashi

A farkon makon nan mu ka ji cewa Babban Bankin Najeriya CBN ya kara dumbuzo makudan Miliyoyin Daloli a kasuwar canji domin a samu sa'ida ga masu bukatar Dalar Amurka.

CBN ta saki Dala Miliyan 210 a kasuwar canji a makon yau
An watso makudan Miliyoyi kasuwar canji

CBN ta ware Dala Miliyan 210 ne a kasuwar canji a makon nan inda daga ciki aka ware Dala Miliyan 100 ga masu neman a dalolin kan sari. An kuma ware Sala Miliyan 55 ne ga masu kananan hannun hari na kasuwanci a Kasar.

KU KARANTA: Kasashen da su ka fi kowane karfi a Duniya

Kamar yadda mu ka samu labari daga manema labarai na kasar, an kuma ware wasu Dala Miliyan 55 ga masu bukatar Dalar Amurka wajen fita Kasashen waje domin neman magani ko karatu da ma kudin jirgi da sauran hidima.

Wani babban Darekta da ke CBN Isaac Okorafor ya bayyana wannan a jiya. Wadanda su ka nemi Dalolin dai za su karbi abin su ne a yau. Ba dai yau CBN ta fara wannan kokari ba wanda ya sa farashin Dalar Amurka bai yi sama ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng