Shugabannin PDP Sama da 500 Suka Sauya Sheka Zuwa YPP a Jihar Akwa Ibom

Shugabannin PDP Sama da 500 Suka Sauya Sheka Zuwa YPP a Jihar Akwa Ibom

  • Jam'iyyar YPP reshen jihar Akwa Ibom ta bayyana ɗaruruwan shugabanni da jiga-jigan PDP da suka koma cikinta zuwa yanzu
  • Shugaban kwamitin tattara bayanan masu sauya sheƙa, Usenobong Akpabio, ya ce YPP ta kama hanyar nasara a zaɓen 2023
  • Wannan dai na zuwa ne a lokacin da jam'iyyar PDP ke faɗi tashin sasanta tsakanin Wike da Atiku

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Akwa Ibom - Jumullan shugabannin PDP 580 a matakin jiha, gunduma da kananan hukumomi na jihar Akwa Ibom ne suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar Young Progressives Party, YPP, tare da Sanata Bassey Akpan.

Vanguard ta ce Sanata Akpan, mai wakiltar mazaɓar Uyo, ba da jimawa ba aka ayyana shi a matsayin ɗan takarar gwamnan Akwa Ibom karkashin inuwar YPP a zaɓen fidda gwanin da aka canza.

Lamarin sauya sheƙa a Siyasar Najeriya.
Shugabannin PDP Sama da 500 Suka Sauya Sheka Zuwa YPP a Jihar Akwa Ibom Hoto: Vanguardngr.com
Asali: UGC

Shugaban kwamitin tattara bayanan masu sauya sheka na YPP, Barista Usenobong Akpabio, shi ne ya bayyana jumullan waɗan da suka rungumi YPP a jihar zuwa yanzun.

Kara karanta wannan

Zamu Ganar da Yan Najeriya, Basu da Zaɓin da Wuce Tinubu da Shettima a 2023, Adamu

A kalamansa, Akpabio, ɗan takarar Sanatan Akwa Ibom ta yamma maso gabas a inuwar YPP, ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Zuwa yanzun an tabbatar da Sanata Bassey Akpan a matsayin ɗan takarar gwamna na YPP, mun so nuna su baki ɗaya (waɗan da suka sauya sheka) amma babu halin hakan, na iya ƙidaya masu muƙamai 580."
"Har yanzun suna cigaba da shigowa jam'iyyar mu, da yawan masu rike da muƙaman PDP na ta ficewa. Kamar ranar Litinin 15 ga watan Agusta, Shugabanni biyu da shugabar mata daga Onna suka fice PDP, suka dawo cikin mu."
"Ina da bayanan su baki ɗaya da takardun murabus ɗin su, a hukumance sun zama mambobin YPP. Muna cigaba da rijistar yan jam'iyya, jiga-jigan PDP na cigaba da sauya sheka a sassan kananan hukumomin jihar nan."

Yan majalisun PDP sun bi sahu zuwa YPP

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Dira Jihar Ogun, Zai Sa Labule da Tsohon Shugaban Ƙasa Kan Muhimmin Abu

Bugu da kari, Akpabio ya bayyana cewa bayan waɗan nan, yan majalisar dokokin jihar Akwa Ibom guda uku sun sauya sheƙa daga PDP zuwa YPP.

"Tsohon kwamishinan ayyuka wanda daga baya ya koma shugaban ma'akatan fadar gwamnati, Ephraim Inyang, da kuma kwamishinan kwadudo da ya yi murabus a watan Maris, Sunny Ibuot, sun koma YPP."

A cewarsa, wasu hadiman gwamna da suka yi murabus daga kan muƙaman su a watan Yuni, sun rungumi jam'iyyar YPP.

A wani labarin kuma Yan majalisu biyu da Dubbannin yan siyasa sun sauya sheka zuwa PDP a gangamin Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karbi dubbannin mambobin jam'iyyu da suka koma PDP a Adamawa.

Atiku Ya kai ziyara mahaifarsa a karon farko tun bayan lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel