Sheriff Modu, Jigon APC a Borno Ya Sauya Sheka, Ya Koma Jam’iyyar PDP

Sheriff Modu, Jigon APC a Borno Ya Sauya Sheka, Ya Koma Jam’iyyar PDP

  • Jigon APC, kuma dan takarar majalisar jiha ya kaura daga jam'iyyar, ya buya a inuwa jam'iyyar PDP mai adawa
  • 'Yan siyasa a kasar nan na yawan sauya sheka a daidai lokacin da ake ci gaba da shirin zaben 2023 mai zuwa
  • Da yake bayyana ficewarsa daga APC, Modu ya bayyana irin gogewar da ya samu a jam'iyyar, kuma zai yi aiki don habaka PDP a gaba

Bama, jihar Borno - Yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa, jigo kuma sakatare a jam'iyyar APC mai mulki ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Yusuf Sheriff Modu, dan takarar ne majalisar jiha a jihar Borno, kuma sakataren shiyyar Arewa maso Gabas a jam'iyyar APC, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Majiya ta ce, ya bayyana ficewarsa ne a wata wasika mai kwanan watan 16 ga Agusta, ya kuma aika ta ne ga Alhaji Babagana Kulami, shugaban jam'iyyar APC na Buduwa Bula Chira na Banki, karamar hukumar Bana ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

2023: Jigon Jam'iyyar APC A Arewa Ya Sauya Sheka Zuwa Labour Party Ta Peter Obi, Ya Bayyana Dalili

Jigon APC ya sauya sheka zuwa PDP a jihar Borno
Sheriff Modu, jigon APC a Borno ya sauya sheka, ya koma jam'iyyar PDP | Hoto: Sherrif Banki
Asali: Facebook

Ya kuma bayyana dalilansa na yanke wannan shawara mai girma na barin APC, inda ya yi alkawarin amfani da gogewar da ya samu a APC wajen habaka jam'iyyar da zai koma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Na yanke shawara mai kyau, inji Modu

Ya yada batun ficewarsa a APC a shafinsa na Facebook a ranar Laraba 17 ga watan Aguta, inda ya rubuta cewa:

“Bismillahi Rahmani Rahim. Lokaci ya yi da zan bude sabon shafin rayuwata….Na san wasu daga masoya na za su yi farin ciki, wasu kuma za su ji bakin ciki. Koma dai yaya ne, ya yanke shawara mai kyau da ta dace.
“A matsayina na mamban jam’iyya na tsawon shekaru takwas, na ba da gudunmawa ainun ga nasarar APC a kasar nan, tun matakin unguwa, kamarar hukuma, jiha, har ma da kasa wanda kowa zai iya tabbatar da hakan a cikin shugabannin jam’iyyar."

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku Da Wike: "Shedan Ya Shigo Jam'iyyar Mu", Jigon Jam'iyyar PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Yi Gargadi

Daga wasikar da ya yada a Facebook kuma wakilin Legit.ng Hausa ya samu, gogaggen matashin dan siyasar ya bayyana irin mukaman da ya rike a APC da kuma kujerun da ya nema a jam'iyyar.

2023: Jam'iyyar APC ta fara kokarin hana guguwar sauya sheka ta yi awon gaba da Mambobinta a Kebbi

A wani labarin, jam'iyyar APC ta soma shirin daƙile yunkurin guguwar sauya sheƙa na ɗibar jiga-jigai da mambobinta zuwa babbar jam'iyyar hamayya PDP a jihar Kebbi.

Daily Trust ta ruwiato cewa jam'iyyar ta kira taron masu ruwa da tsaki domin sasanta wa da mambobi waɗan da suka fusata da nufin daƙile yunkirinsu na sauya sheƙa.

Ba da jimawa ba jam'iyyar APC ta yi rashin wasu manyan jiga-jiganta zuwa tsagin hamayya bisa dalilai daban-daban duk a jihar ta Kebbi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel