Abin da ya wakana: Shugaban Majalisa Ya Fadi Alkawarin da Obasanjo Ya yi wa Tinubu

Abin da ya wakana: Shugaban Majalisa Ya Fadi Alkawarin da Obasanjo Ya yi wa Tinubu

  • Femi Gbajabiamila wanda shi ne Shugaban Majalisa ya fadi abin da ya wakana da Bola Tinubu ya ziyarci Olusegun Obasanjo a gidansa
  • Shugaban Majalisar Wakilan Tarayyar yace Olusegun Obasanjo ya rungumi ‘dan takararsu, ya nuna masu zai kai ga nasara a zaben 2023
  • Gbajabiamila ya nuna cewa zaben shugaban kasa mai zuwa zai kasance tsakanin mutum uku ne, ya kuma ce Bola Tinubu ya fi cancanta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya yi karin haske a kan haduwar Asiwaju Bola Tinubu da Cif Olusegun Obasanjo.

Rahoton The Cable na ranar Alhamis, 18 ga watan Agusta 2022, ya nuna Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yi wannan magana ne da ya je Legas.

A cewar Gbajabiamila, tsohon shugaban kasar ya yi wa Tinubu alkawarin kai shi ga nasara a 2023.

Kara karanta wannan

Bayanin Zuwan Bola Tinubu Gidan Olusegun Obasanjo a jihar Ogun Ya Bayyana

A ranar Alhamis ne Gbajabiamila ya zanta da mutanen mazabarsa a Surulere a wajen wani gangami na APC, inda ya samu kyakkyawar tarba a gida.

A cewar ‘dan siyasar, Obasanjo ya yi wa Tinubu addu’ar Ubangiji ya ba shi nasara a zaben 2023. Jaridar Vanguard ta bayyana wannan a rahotonta.

Tawagar Tinubu tayi mamaki

Gbaja kamar yadda a kan kira sa, ya fada, ba su yi nufin mutane su san da labarin Tinubu zai ziyarci Obasanjo ba, don haka aka tafi da mutum takwas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gbaja a gidan Obasanjo
Tinubu, Obasanjo da Gbaja Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Ko da aka isa gidan tsohon shugaban na Najeriya, sai jama’an Asiwaju Tinubu suka ga abin mamaki, dinbin masoya sun cika gidan, ana sauraron zuwansu.

Gbajabiamila yace wannan ya sa aka zabi mutum uku daga kowane bangare biyun domin a sa labule. Sai Tinubu ya dauki Gbajabiamila, Osoba da Akande.

Kara karanta wannan

Rigimar Gidan PDP Ta Cabe da Fitowar Tsohon Bidiyon Shugaban Jam’iyya

“Obasanjo ya yi magana mai tsawo, kuma duk mun yi farin ciki. Ya karbi ‘dan takararmu kamar ‘danuwansa, ya karfafa masa gwiwa, ya yi masa addu’a.”

- Femi Gbajabiamilla

Tinubu ya fi kowa cancanta

“Bisa dukkan alamu manyan ‘yan takara uku ne a zaben 2023. Mun san tarihin kowane, mun san abubuwan da suka yi, mun san abubuwan da su yi ba.
“Biyu tsofaffin gwamnoni ne kuma mun san wanda ayyukansa suka dore. Mun san yadda sauran biyu suka kare a ofis, babu wanda ya fi Tinubu kokari.”

- Femi Gbajabiamilla

Jirgin Tinubu ya sauka a Abeokuta

A tsakiyar makon nan ne aka ji labari tsohon gwamnan Legas watau Tinubu ya je gidan Olusegun Obasanjo. An san ‘yan siyasar ba aminan juna ba ne.

Kun ji Femi Gbajabiamila, da Cif Bisi Akande da Malam Nuhu Ribadu sun takawa ‘Dan takaran APC baya zuwa gidan tsohon shugaban kasar da ke Ogun.

Kara karanta wannan

Karar kwana: Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa IBB ya rigamu gidan gaskiya

Gwamna Dapo Abiodun, Segun Osoba, Gbenga Daniel da Hon. Olakunle Oluomo suka tarbe su.

Kwana guda da yin zaman, sai shugaban majalisar ya shaidawa Duniya cewa Obasanjo ya fadi abubuwan yabo a game da takarar da mai gidansu yake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel