Kwankwaso Ya yi Nadin Mukamai a Shirin Takarar Shugaban kasa a NNPP
- Rabiu Musa Kwankwaso ya nada wadanda za su rika magana da yawun kwamitin kamfe dinsa
- ‘Dan takaran Shugaban kasar na zaben 2023 ya bada wannan sanarwa ne a shafinsa na Twitter a jiya
- Tsohon ‘Dan majalisar Tarayya, Abdulmumin Jibrin da Barr. Ladipo Johnson sun zama kakakin kamfe
Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso ya amince da nadin wadanda za su rika magana da kwamitin yakin neman takarar shugaban kasa da yake yi.
Mun ji cewa wannan sanarwa ta fito daga bakin shi kan sa Rabiu Musa Kwankwaso a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, 17 ga watan Agusta 2022.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya zabi Hon Abdulmumin Jibrin da Barr. Ladipo Johnson su zama kakakin kwamitin yakin takaran da yake yi a NNPP.
‘Dan takaran shugaban kasar yake cewa yana da tabbacin Jibrin da Johnson za su yi amfani da kwarewarsu wajen kai jam’iyyar NNPP ga nasara.
“Na amince da nadin Hon Abdulmumin Jibrin da Barr. Ladipo Johnson a matsayin kakakin kwamitin yakin neman zabe na.
Ba na shakkar cewa wadannan biyu za su yi amfani da kwarewarsu wajen sadarwa da sanin mutanen wajen kafa sabuwar Najeriya.”
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
- Rabiu Musa Kwankwaso
Kamar yadda hadimin ‘dan takarar, Saifullahi Hassan ya bayyana a wani jawabi da ya fitar, Jibrin tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayya ne a Najeriya.
Baya ga zamansa ‘dan siyasa, Hon. Jibrin masani ne a kan harkar hulda da jama’a wanda ya yi digiri a fannin siyasa da ilmin huldar kasashe waje.
Sabon kakakin ‘dan takaran ya yi digirin B. Sc, M. Sc da PhD daga ABU Zaria da Jami’ar Abuja, sannan ya yi kwas kwas a Harvard da SBS Zurich.
Shi kuwa Ladipo Johnson kwararren Lauya ne wanda yake aiki da Agbese & Johnson a Legas.
Baraka a NNPP
Mun samu labari cewa Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce tsakaninsa da mutanen Sanata Ibrahim Shekarau babu wata rigima kamar yadda ake fada.
‘Dan takaran shugaban kasar na NNPP ya shaidawa ‘yan jarida haka. Kwankwaso ya fadi abin da ya sa ba su iya biyawa tsagin Shekarau bukatunsa ba.
Asali: Legit.ng