Babu Baraka a NNPP: Kwankwaso Yace Shi da Shekarau Suna Tare Daram-Dam

Babu Baraka a NNPP: Kwankwaso Yace Shi da Shekarau Suna Tare Daram-Dam

  • Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce tsakaninsa da mutanen Sanata Ibrahim Shekarau babu wata rigima
  • ‘Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar NNPP ya shaidawa ‘yan jarida haka a wata hira da ya yi
  • Ana rade-radin tsohon gwamnan Kano watau Ibrahim Shekarau zai fice daga NNPP bayan kwanaki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Rabi'u Musa Kwankwaso ya shaidawa Duniya cewa a halin yanzu babu wata rigima da ake yi tsakaninsa da tsaginsu Malam Ibrahim Shekarau.

A ranar Laraba, 17 ga watan Agusta 2022, BBC Hausa ta zanta da Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda ya yi karin haske a kan tafiyar jam’iyyar NNPP.

Rabiu Kwankwaso ya yi watsi da rade-radin da ake yi cewa babu zaman lafiya a NNPP tsakanin mutanensa da kuma ‘yan bangaren Sardaunan Kano.

Jita-jitar rabuwar kai da barazanar barin NNPP da su Shekarau suke yi ya je kunnen Kwankwaso, wanda ya shaida cewa ba haka gaskiyar lamarin yake ba.

Kara karanta wannan

Zan Yanke Hukunci Kan Ko Zan Fice Daga Jam'iyyar Kwankwaso A Wannan Makon, Shekarau Ya Magantu

An saba yarjejeniya da Shekarau?

‘Dan siyasar ya fadawa BBC cewa ba a kulla wasu yarjejeniya wajen jawo Malam Shekarau zuwa NNPP ba, sai dai ya ce akwai bukatun da aka gabatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda jagoran na NNPP na kasa ya fada, bangaren Sanatan na Kano ta tsakiya ba su gabatar da bukatunsu a kan kari, a lokacin da ya dace ba.

Kwankwaso Yace Shi da Shekarau Suna Tare
Malam Shekarau da Kwankwaso Hoto: BBCNewsHausa
Asali: UGC

‘Dan takarar shugaban kasar a inuwar NNPP yace an yi bakin kokarin biyawa bangaren Sanata Shekarau bukatun tsayawa takara, amma lokaci ya matse,

Saboda akwai wa’adin da hukumar zabe ta bada domin kammala tsaida gwani, ba duka bukatun su Shekarau ne jam’iyyar NNPP ta iya biya masu a Kano ba.

Hakan ba zai yi tasiri a NNPP ba

Kwankwaso yace wannan matsala da aka samu ba za ta taba alakar da ke tsakaninsa da Shekarau ba. Sahelian Times ta fitar da irin wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Karon Farko a Tarihi, Buhari Ya Kirkiro Sabon Mukami Domin Magance Rashin Tsaro

Sanata Kwankwaso ya yi alkawarin idan NNPP ta karbi gwamnati, za a warewa mutanen da ke tare da tsohon abokin adawarsa mukamai masu tsoka.

Wasu daga cikin ‘yan tsagin Malam Shekarau su na kukan an yi watsi da su a tafiyar NNPP a Kano, sun ce ‘Yan Kwankwasiyya ne kadai ake damawa da su.

Sha'aban Sharada ya bar APC

A jiya kun ji labari cewa zaman Sha’aban Ibrahim Sharada a jam’iyyar APC ya zo karshe. 'Dan majalisar zai yi takarar kujerar Gwamnan Kano ne a ADC.

Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharada ya sauya-sheka daga APC mai mulki ne bayan tsawon lokacin bangarensu na G7 suna rigima da gwamnatin Ganduje.

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel