Jerin Manyan Mukamai 15 Masu Gwabi Da El-Rufai Da APC Ta Arewa Maso Yamma Suka Nema Daga Wurin Tinubu
- Jiga-Jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na arewa maso yamma suna son jam'iyyar da Tinubu su tanadar musu wasu manyan mukamai
- A cewar jiga-jigan jam'iyyar, suna son wannan mukaman ne a madadin goyon baya da za su bada don ganin jam'iyyar ta ci zaben shugaban kasa na 2023
- Wasu daga cikin mukaman sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, ministan kudi da wasu mukamai masu gwabi
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, kamar yadda aka rahoto ya jagoranci gabatar da wata takarda daga jiga-jigan APC na Arewa maso Yamma ga Bola Ahmed Tinubu.
Yankin na arewa maso yamma ta bukaci dan takarar shugaban kasar jam'iyyar da shugabannin jam'iyyar su bawa yankin wasu mukaman siyasa.
A cewar yan yankin, suna son wannan alfarmar ne idan ana son goyon bayansu don ganin jam'iyyar ta ci zaben shugaban kasa na 2023.
Rikicin Atiku Da Wike: "Shedan Ya Shigo Jam'iyyar Mu", Jigon Jam'iyyar PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Yi Gargadi
A takardar, yankin ta ce saboda muhimmancinta da gudunmawa da za ta bada a zaben da ke tafe, ya kamata a ware wa yankin dukkan muhimman mukamai.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Amma dan takarar shugaban kasar na APC ya yi gaggawa ya zabi mataimakinsa, duk da cewa ya san da maganan bukatun.
Ga jerin manyan mukaman da arewa maso yamma ke so kamar yadda Jaridar Vanguard ta wallafa.
- Mataimakin shugaban kasa
- Sakataren Gwamnatin Tarayya
- Ministan Kudi
- Ministan Ayyuka
- Ministan Noma
- Ministan Abuja
- Ministan Harkokin Cikin Gida
- Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro
- Shugabancin hukumar NIMASA
- Shugabancin Hukumar Kula Da Tashohin Jiragen Ruwa, NPA
- Bankin Bada Tallafi Da Jarin Noma, NIRSAL
- Bankin Manoma (BOA)
- Bankin Masana'antu (BOI)
- Shugabancin DSS
- Shugabancin hukumar SMEDAN
Legit.ng Hausa ta tuntubi wani jigon jam'iyyar APC a Kaduna ta Kudu domin samun karin bayani game da wannan bukata da aka ce yan arewa maso yamman sun gabatarwa, Bola Tinubu.
Jigon, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce kamun ƙafa a siyasa wato a turance 'lobbying' ba sabon abu bane a musamman idan zaɓe ya ƙarato.
"Shi harka na siyasa haka ya gada, yankin area maso yamma ta saba taka rawa mai muhimmanci a ga nasarar jam'iyyar APC.
"Don haka ba laifi bane idan an nemi ɗan takarar shugabancin kasa ya yi wa yankin tukwici bisa karamcin da ya saba yi yayin zaɓe," in ji shi.
Da aka masa tambaya shin ko Tinubun ya amince da dukkan bukatunsu, ya ce:
"Na yi imanin dan takarar shugaban kasar mu ya san muhimmancin yankin na arewa maso gabas don haka ba zai ƙi sauraron bukatun mu ba."
2023: Bayan Atiku, Tinubu Shima Yana Zawarcin Shekarau, Za Su Gana Ranar Laraba
A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya gayyaci tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, zuwa taro a ranar Laraba, kwararan majiyoyi suka shaidawa Daily Nigerian.
Shekarau Zai Fita Daga NNPP Ta Kwankwaso Ya Koma PDP Saboda Wasu Alƙawurra 'Masu Tsoka' Da Atiku Ya Masa
Dan takarar shugaban kasar na APC ya gayyaci Shekarau, wanda shine dan takarar sanata na jam'iyyar NNPP, zuwa taro don zawarcinsa ya dawo jam'iyyarsa.
Shekarau ya riga ya cimma yarjejeniya da dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar cewa zai koma jam'iyyarsu a nada shi shugaban kamfen na Arewa maso Yamma, rahoton Daily Nigerian.
Asali: Legit.ng